Gwamnatin Kaduna za ta rugurguza gadar sama dake Kawo don gina sabuwa

Gwamnatin Kaduna za ta rugurguza gadar sama dake Kawo don gina sabuwa

Gwamnatin jahar Kaduna a karkashin jagorancin Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai ta kammala shirye shiryen kwance gadar sama dake Kawo gaba dayanta tare da maye gurbinta da wata sabuwa ta zamani da ta fita girma.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban hukumar kula da hanyoyin jahar Kaduna, KADRA, Injiniya Mohammed Lawal ne ya bayyana haka a karshen makon data gabata yayin da yake ganawa da al’ummar yankin Kawo.

KU KARANTA: Kowa ya bar gida, gida ya bar shi: Atiku zai dawo Najeriya ranar da ya cika shekaru 73

A jawabinsa, shugaban KADRA, Mohammed Lawal ya bayyana cewa za’a rushe iya gadar ne kawai, amma ba za’a rushe pilolin da suka rike gadar ba saboda suna da karfinsu har yanzu, don haka saman kawar za’a kwashe tare da sabunta shi da kuma kara wasu sassa daban daban.

Lawal yace a yadda gadar Kawo take a yanzu ta yi ma motocin dake hawa kanta kadan, don haka gwamnati za ta gina karin tituna da karin shataletale guda uku a kasan gadar, sa’annan yace zasu samar da wasu hanyoyin da masu ababen hawa zasu bi iya watanni 20 da za’a yi ana aikin.

“Zamu bude hanyar juyawa a kan titin Kawo kafin a kai gadar, ta yadda ba sai motoci sun shiga kasar gadar kafin su juyo ba, titin Lafiya Road kuma zai zamo hanyar da mutanen Kawo zasu bi idan zasu shiga cikin gari.” Inji shi.

Daga karshe shugaban KADRA ya tabbatar da cewa gwamnati za ta biya kudin diyya ga duk wadanda aikin ginin ya shafa matukar suna da inganatattun takardun kadarorinsu da za’a rusa.

Shi ma a nasa jawabin, hakimin Kawo, Alhaji Jibrin Magaji ya bayyana cewa rashin sanya jama’an yankin a cikin aiki ne ya janyo aikin baban giwan da aka yi a baya, amma a yanzu ya yi ma gwamnan Kaduna godiya daya kirkiri wannan aikin, inda yace aiki ne da zai shafi yankin Arewa gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel