Bidiyon CCTV ta nuna ma'aikatan banki suna wawushe kudi kafin 'yan fashi su iso - 'Yan sanda

Bidiyon CCTV ta nuna ma'aikatan banki suna wawushe kudi kafin 'yan fashi su iso - 'Yan sanda

Asuquo Amba, kwamishinan 'yan sanda na jihar Ekiti ya ce na'urar daukan bidiyon sirri na CCTV ta nuna cewa wani ma'aikacin bankin yana daukan kudade daga dakin ajiyar kudi na bakin wasu 'yan mintina kafin 'yan fashin su kai hari a bankin.

'Yan fashin sun harbe wani jami'in dan sanda da wata karamar yarinya a yayin da suka kai hari a bankin a ranar Alhamis a karamar hukumar Oye-Ekiti na jihar.

A yayin da ya ke tsokaci kan afkuwar fashin a ranar Juma'a, kwamishinan 'yan sandan ya ce akwai alamar kaman 'yan fashin sun hada kai da wasu ma'aikatan bankin.

Amba ya ce 'yan fashin sun fara zuwa ofishin 'yan sanda dake garin suka kai hari sannan suka karasa zuwa bankin inda suka yi awon gaba da kudi fiye da miliyan 25.

Ya kara da cewa sufeta janar na rundunar (IGP) Mohammed Adamu ya bayar da umurnin yin bincike a kan afkuwar lamarin.

DUBA WANNAN: Alkali ya ja kunne a kan 'wasan kwaikwayo' da Maina ke yi a kotu

Ya ce, "IGP ya bayar da umurnin yin cikakken bincike a kan lamarin kuma ya ce dole a kawo karshen afkuwar irin wannan barnar."

Amba ya ce 'yan sandan sun gano wani kwali da aka boye kudi fiye da miliyan 2 a bankin kafin fashin.

Ya ce, "Duk da cewa sun samu damar tserewa, babu wanda ya yi kokarin ya gudu, suna ta tattara kudi ne kawai kuma wannan hujja ce."

"Ma'aikacin bankin ya bude asusun ne misalin karfe 3.05 su kuma 'yan fashin sun fasa kofar dakin ajiyar misalin karfe 3.12, wannan alama ce da ke nuna akwai hadin baki tsakanin 'yan fashin da wasu a bankin.

"An boye kwallin kudin a kasan tabur a cikin zauren bankin. Akwai yiwuwar kudin yana daga cikin wadanda aka kwaso ne daga dakin ajiyar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel