Yan bindigan dake fitinar jahar Zamfara abokanka ne, ka sansu – Yari ga Matawalle

Yan bindigan dake fitinar jahar Zamfara abokanka ne, ka sansu – Yari ga Matawalle

An yi cacar baki, nuna ma juna yatsa tare da murza gashin baki tsakanin tsohon gwamnan jahar Zamfara Abdul Aziz Yari da gwamnan jahar Bello Matawalle biyo bayan sabbin hare hare da aka kaddamar a jahar a yan kwanakin nan bayan tsawon lokaci ana zaman lafiya.

Cikin wani bidiyo daya karade shafukan sadarwa, an jiyo gwamnan jahar yana zargin Abdulaziz Yari da shirya hare haren da ake kaiwa jahar Zamfara, har ma ya yi barazanar kama shi da hannunsa idan har aka sake kai hari wani wuri a Zamfara.

KU KARANTA: Janar Buratai ya gyara firamarin da ya yi a Kaduna, ya bata kyautan littafai 1000

Sai dai tsohon gwamna Yari ya mayar da martani ga Gwamna Matawalle, inda yace gwamnan ya fi kowa sanin yan bindigan da suka kai hari kauyen Karaye saboda abokanansa ne na kud da kud.

A wani hari da aka dade ba’a samu irinsa ba a jahar Zamfara, wasu yan bindiga dadi sun kai hari kauyen Karaye dake cikin karamar hukumar Gummi na jahar Zamfara inda suka kashe mutane 14, a ranar Lahadin da ta gabata.

A dalilin harin ne Gwamna Matawalle yace: “Na rantse idan Abdulaziz Yari ya sake zuwa garin nan har aka samu tashin hankali, sai na kama shi da kaina, har kauyensa Talatan Mafara zan bi shi na kamashi, ba kuma da wasa nake ba.

“Wannan shi ne karo na uku da ake samun matsalar tsaro a duk lokacin daya kawo ziyara jahar nan, nasarar da muka samu wajen shawo kan matsalar tsaro nasara ce daga Allah, ba kuma zan tsaya tsohon gwamna da abokansa su lalata ma aiki ba, zan nuna masa ni ke da karfin mulki ba shi ba.” Inji shi.

Sai dai cikin martanin da Yari ya mayar yayin tattaunawa da jaridar Daily Nigerian, yace: “Gwamnan ya je ya duba kundin tsarin mulki ya ga idan yana da daman kamani don kawai na kaiziyara jahata, idan har ziyarar da nake kaiwa gida ne yake kawo tashin hankali, me yasa ba’a samu a Talatan mafara ba?

“Ni ba sa’ansa bane a siyasance, na fi karfinsa, lokacin da nake gwamna ya yi kadan na ganshi koda a cikin mafarkina, a duk bayan kwanaki 30 ko 40 nake zuwa gida domin ganawa da yan uwa, shuwagabannin addinai, abokan siyasa, yan kasuwa da sauransu, don haka yake bakin cikin matsayina a Zamfara.” Inji shi.

Daga karshe Yari ya yi zargin babu zaman lafiya a jahar Zamfara saboda gwamnan ya san ko su wanene suke kai hare haren dake kashe jama’an jahar Zamfara saboda abokansa ne.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel