Yan bindiga sun kai farmaki jahar Filato, sun kashe shugaban Miyetti Allah

Yan bindiga sun kai farmaki jahar Filato, sun kashe shugaban Miyetti Allah

Wasu gungun yan bindiga sun kaddamar da hari a karamar hukumar Mangu inda suka kashe shugaban kungiyar Fulani makiyaya na Miyetti Allah reshen karamar hukumar, Sa’adu Musa Julde.

Jaridar Blue Print ta ruwaito yan bindigan sun kaddamar da harin ne a daren Laraba, 20 ga watan Nuwamba, inda suka bindige Ardo Sa’adu Musa Julde, sa’annan suka tsere cikin daji ba tare da an kama ko mutum daya daga cikinsu ba.

KU KARANTA: Abbas Abubakar ya bayyana abin da yasa ya kashe matar kawunsa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, wanda kuma shine shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jahar Filato, Malam Muhammad Nura Abdullahi ya tabbatar da kisan Ardo Sa’adu a shafinsa.

“Wannan shi ne gawar Ardo Sa’adu Musa Julde dake lardin Gidniri, kuma shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen karamar hukumar Mangu, ya mutu a sanadiyyar rauni daya samu sakamakon harbinsa da wasu yan bindiga suka yi.

“Da misalin karfe 8:47 na daren Laraba yan bindigan suka bindigeshi a daidai garejin yan tipa dake kusa da ofishin Yansanda, amma har yanzu ba’a kama ko mutum daya dake da hannu cikin kisan ba.” Inji shi.

A wani labarin kuma, wani matashi dan shekara 20, Abbas Abubakar mazaunin kauyen Kissayip cikin karamar hukumar Bassa ta jahar Filato ya bayyana ma duniya dalilin da yasa ya kashe matar kawunsa.

Abba ya bayyana cewa ya kashe matar ne sakamakon zarginta da yake yi da kashe wani kawunsa, sa’annan ya kara da cewa ita ce wanda ta kashe masa shanunsa.

Abbas ya bayyana haka ne yayin da Yansanda suka gabatar dasu a gaban manema labaru a babban ofishin Yansandan jahar Filato a ranar Alhamis, 21 ga watan Nuwamba, inda yace matar ta tabbatar da kisan kawun nasa ta hanyar cika baki da nuna isa, sa’annan ta yi barazanar kashe shi shi ma, da danginsu duka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel