Buhari ya yi wa Atiku ta'aziyyar rasuwar shakikin hadiminsa, Umar Pariya

Buhari ya yi wa Atiku ta'aziyyar rasuwar shakikin hadiminsa, Umar Pariya

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a kan rasuwar tsohon hadiminsa na kut-da-kut, Umar Pariya.

Shugaban kasar ya wallafa wannan sakon ta'aziyyar ne ta shafinsa na Twitter @Mbuhari

A sakon ta'aziyarsa kan rasuwar, Shugaba Buhari ya ce: "Na yi juyayin samun labarin rasuwar shakikin hadiminka, Alhaji Pariya.

"Rasa shakiki da aka kwashe shekaru tare abu ne mai matukar sosa zuciya. Ina addu'ar Allah Ubangiji ya baka hakurin jure rashinsa.

"Allah ya kuma bawa iyalansa hakurin rashinsa, ya yafe masa kurakurensa ya kuma saka masa a kan ayyukansa na alheri a gobe kiyama."

DUBA WANNAN: Zaben Kogi: 'Yan daba sun kona shugaban mata na PDP a gidanta

Mista Pariya ya rasu ne a ranar Talata a wani asibiti dake birnin Dubai bayan fama da rashin lafiya.

Atiku Abubakar ya yi takarar zabe na kujerar shugaban kasa da Buhari inda ya sha kaye kamar yadda sakamakon da Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta fitar suka nuna.

Bayan bayyana sakamakon zaben, tsohon mataimakin shugaban kasar da ya yi takara a karkashin inuwar jam'iyyar PDP ya garzaya kotu domin kallubalantar nasarar Buhari.

Sai dai Atiku Abubakar bai samu nasara ba a kotun zabe da kotun koli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel