Kano: Budurwa ta yi yunkurin rungumar taransufoma bayan anyi mata auren dole da dan shekara 70

Kano: Budurwa ta yi yunkurin rungumar taransufoma bayan anyi mata auren dole da dan shekara 70

- A ranar Juma’ar da ta gabata ne wata matashiya ta yi yunkurin shiga na’urar da ke bada wutar lantarki wato taransufoma

- Matashiyar ta sanar da mazauna yankin da taransufomar ta ke, cewa an aura mata tsoho ne kuma bata so

- Kungiyar kare hakkin dan Adam karkashin shugabancin Karibu Lawan Kabara ta sha alwashin kwato mata hakkinta

Al’amarin ya faru ne a ranar Juma’a da ta gabata, 15 ga wannan watan da muke ciki na Nuwamba. Wata matashiya ce ta yi yunkurin shiga cikin na’urar da ke bada hasken wutar lantarki wato taransufoma.

Wannan lamari dai ya faru ne a unguwar Sharada da ke yankin karamar hukumar birnin Kano bayan da ta yo tattaki tun daga unguwar Rimin Kebe da ke yankin karamar hukumar Ungogo.

Daya daga cikin wadanda suka kaiwa matashiyar dauki yace, ta samesu da koken cewa an yi mata auren dole ne da wani tsoho da bata so. A don haka ne take bukatar mafita.

KU KARANTA: Jerin sunayen ’ya’yan marigayi Sarkin Kano Alhaji Dr. Ado Bayero guda 62

Mazauna yankin sun kara da cewa, tana gama fada musu hakan sai ta nufi dakin da na’urar bada wutar lantarkin ke ciki don kawo karshen rayuwarta. Sai dai sun yi gaggawar hana ta shiga.

Ganin wannan yunkurin ne yasa kungiyar kare hakkin dan Adam ta shiga lamarin. Shugaban kungiyar, Karibu Lawan Kabara, ya bayyana cewa zasu yi iyakar bakin kokarinsu wajen ganin sun kwato wa matashiyar hakkinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel