Siyasa mugun wasa: An banka wuta a azuzuwan daukan darasi da Dino Melaye ya gina ma jama’a

Siyasa mugun wasa: An banka wuta a azuzuwan daukan darasi da Dino Melaye ya gina ma jama’a

Wasu yan bangan siyasa sun kai samame zuwa wasu sabbin azuzuwan dalibai da Sanata Dino Melaye ya gina kyauta domin amfanin jama’an mazabarsa, inda suka banka musu wuta, suka kone kurmus!

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito a yayin wata ziyara daya kai makarantar da lamarin ya faru a cikinta, watau Sakandarin sarkin noma dake cikin garin Lokoja, Dino ya bayyana cewa zai sake gina azuzuwan nan take.

KU KARANTA: Yansanda sun kama Magidanci da laifin kashe makwabcinsa a kan ‘musu’

Haka zalika Dino ya dauki alwashin babu wata barazana da za ta dakatar da shi daga gudanar da ayyukan cigaba domin amfanin jama’ansa. Ita ma gwamnatin jahar ta yi Allah-wadai da wannan lamari, haka zalika Gwamnan jahar Yahaya Bello ya umarci rundunar Yansandan jahar ta kamo duk masu hannu cikin ta’asan.

A wani labarin kuma, hukumar zabe mai zaman kan ta ta Najeriya, INEC ta bayyana cewa babu wanda ya yi nasara a zaben kujerar majalisar dattawa dake wakiltar jama’an mazabar Kogi ta yamma a zaben da ta gudanar a ranar Asabar ba.

INEC ta bayyana haka ne sakamakon tazarar dake tsakanin dan takarar APC wanda ya ke kan gaba, Smart Adeyemi, da kuma Sanata mai-ci, Dino Melaye, bai kai yawan kuri’un da aka soke a mazabar ba.

An soke zabe a akwatuna har 53 da ke cikin rumfunan zabe 20 da ke fadin yankin Yammacin jihar Kogi a zaben karshen makon jiya. Wannan ya sa aka kashe kuri’u 43, 127 inji hukumar INEC.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel