Kwarto ya yiwa mata da miji dukan tsiya a Kano bayan ya kasa samun biyan bukata

Kwarto ya yiwa mata da miji dukan tsiya a Kano bayan ya kasa samun biyan bukata

- Wani magaidanci da matarsa sun fada mummunan hali sakamakon kutsen da wani mutum ya yi musu

- An zargi Sulaiman Saleh da fadawa gidan Mallam Bello kwartanci a ranar Litinin dinnan da ta gabata

- Rashin samun nasara ne yasa ya yi amfani da wukarsa wajen yankar ma’auratan a wuya, hannaye da wasu sassan jikinsu

Wani magidanci mai suna Mallam Bello da mai dakinsa sun fada wani mummunan hali, yayin da wani mutumi mai suna Sulaiman Saleh ya yankesu da wuka a wuya, hannaye da wasu sassan jikinsu.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin dinnan da ta gabata a kauyen Wutar Kara da ke karamar hukumar Rano ta jihar Kano.

An zargi Sulaiman da kutse a gidan Malam Bello da niyyar afkawa mai dakinsa. Amma sai bai yi nasara ba, saboda matar Mallam Bello ta yi kururuwa wacce ta jawo hankalin mai gidanta ya kawo mata dauki.

KU KARANTA: Tashin hankali: Da kaina na tono gawarwakin mahaifana domin na sayar da kasusuwansu

Wanda ake zargin ya lura hakarsa ba zata cimma ruwa ba shiyasa yayi amfani da makamin hannunshi don raunata ma’auratan. Ya yanki mijin a wuya da hannayensa inda ita kuma matar ya yanketa a wuya da sassan jikinta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Kiyawa ya tabbatar da aukuwar wannan lamarin. Ya ce, mutanen anguwar sun kaiwa magidancin dauki don har sun lakadawa wanda ake zargin dukan tsiya.

Magidancin a yayin tattaunawarsa da Freedom rediyo, ya bayyana takaicinsa da matukar alhinin faruwar lamarin

A yanzu dai, ‘yan sanda sun mika wanda ake zargin zuwa asibitin Murtala Mohammed da ke Kano. Sun bazama cigaba da bincike ta bangarensu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel