Dalilin sauke mataimakin kakakin majalisar jihar Gombe

Dalilin sauke mataimakin kakakin majalisar jihar Gombe

Matsalolin da suka danganta da motocin gwamnati da alawus sune suka kawo sanadin tsige mataimakin kakakin majalisar jihar Gombe, Shuaibu Adama Haruna, kamar yadda jaridar daily Trust ta gano.

Wakilin D ailyTrust ya kawo rahoton cewa, tsaikon da aka samu akan bada ababen hawa 24 ga 'yan majalisar jihar Gombe din ne ya kawo baraka tsakaninsu da Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya.

A cikin 'yan majalisar jihar 24; APC na da mambobi 19 inda PDP ke da 5.

Tun bayan rantsar da su a ranar 14 ga watan Yuni, 'yan majalisar na ta amfani da ababen hawansu ne, duk da kuwa koke kala-kala da suka kaiwa gwamnan don siyen sabbin ababen hawan. 'Yan majalisar sun bayyana yanda suka fi son motocin masu kirar SUV, kamar yadda majiya daga majalisar ta bayyanawa wakilin Daily Trust.

Daya daga cikin majiyar tace, akan haka ne majalisar ta hanzarta tantancewa tare da tabbatar da kwamishinoni 21 da gwamnan ya zaba, masu bada shawara na musamman da kuma kasafin kudin shekara mai zuwa da ya mika ga majalisar.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kone motar 'yan sanda a Kaduna

"Amma kuma gwamnan yaki amincewa da bukatarsu da ke gabansa a kan motocin. A hakan ne kuma'yan majalisar ke amfani da ababen hawansu koda kuwa wajen aikin majalisar ne. Kwatsam! Sai suka gano cewa, Gwamnan ya siyawa sabbin kwamishinonin ababen hawa. Hakan kuwa ya tunzura su,"

Ya kara da cewa, 'yan majalisar suna ta kokarin ganin sun sasanta kansu da gwamnan amma abin ya ci tura don kuwa kowa ya san barakar da ke tsakaninsu.

Duk da banbance-banbancen jam'iyya da ke tsakaninsu, 'yan majalisar sun yi taro inda suka yanke hukuncin gujewa duk wani aiki ko taron da gwamnan ya gayyacesu har zuwa lokaci da zai siya musu ababen hawan. Bayan wannan yarjejeniyar, 'yan majalisar sun ki halartar kaddamar da motocin bas 50 da gwamnan ya ba wa kamfanin sufurin jihar, Gombe Line.

An zargi cewa, tsohon mataimakin kakakin majalisar ya sanar da gwamnan wannan bayani.

A taron rantsar da kwamishinonin jihar da wasu zababbu na jihar da ya gabata a ranar Asabar, babu dan majalisar da ya je sai mataimakin kakakin majalisar kadai, lamarin da ya harzuka sauran 'yan majalisar.

Hakan kuwa ne ya kawo sanadin tsigesa a matsayin mataimakin kakakin majalisar a ranar Talata, aka kuma maye gurbinsa da Sidi Buba, dan majalisa mai wakiltar Kwami ta yamma.

A lokacin da aka tuntubi kakakin majalisar akan dalilinsu na yin hakan, ya ce "Wannan zancen cikin gida ne. Idan lokaci yayi zamu sanar da mutane".

Duk da dai, mai bada shawara ga gwamnan jihar akan sadarwar jama'a, Anas Ibrahim Kubalu, yace tsige mataimakin kakakin majalisar bashi da nasaba da alakar da ke tsakanin mataimakin kakakin majalisar da gwamnan. Ya kara jaddada cewa, babu wata baraka da ke tsakanin gwamnan da 'yan majalisar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel