Manyan sarakunan Afirka 5 da suka mallaki arziki na ban mamaki

Manyan sarakunan Afirka 5 da suka mallaki arziki na ban mamaki

Duk da kudi zasu iya zama tushen kowanne sharri, amma kuma suna da dadi. Muna kokarin ba da dalilai masu tarin yawa da yasa kudi suke zama tushen wasu sharrikan amma kuma nemansu dole ne.

Ga sunayen manyan sarakunan Afirka guda biyar masu tarin dukiya kamar yadda GhanaCelebrities.Com suka wallafa.

5. Otumfuor Osei Tutu II, Ghana

Otumfour basarake ne a Ghana wanda yake jagorantar masarautar Ashanti. An haife shi a watan Mayu, 1950. Ya zama sarki na 16 na masarautar Ashanti bayan da ya gaji sarautar a shekarar 1989. Yana mulkar masarautar Ashanti da ke yankin Ghana wacce ta shahara a hako zinare. Yana da dukiya da ta kai $10million.

4. Sarki Mswati III, Swaziland

Mswati sarkin Swaziland ne . Duk da tarin talaucin da ya yi wa mutanensa katutu, yana daga cikin sarakunan Afirka masu tarin dukiya. Sarki Mswati yana mataki na 4 a jerin sarakai masu arziki. Ya hau mulkin yana da shekaru 18 a duniya kuma har a yau yana nan a karagar. An haife shi a watan Afirilu 1968 a Manzini. Maswati na da dukiyar da ta kai $2million.

DUBA WANNAN: Gwarzon shekara: Wani matashi zai angonce da 'yammata uku rigis (Hoto)

3. Sarki Okunde Sijuwade, Najeriya

Abin alhinin shine, sarki Okunde Sijuwade wanda a ka fi sani da Olubuese II ya rasu a 2015. An haife shi a watan Janairu 1930. Ya mulki masarautarsa da ke Ife a jihar Ogun na shekaru 35. Yana da dukiyar da ta kai $75 million.

2. Sarki Fredrick obateru Akinruta, Najeriya

Shi ne sarkin jihar Ondo. Obateru sananne ne a kan rayuwarsa wacce take cike da izza da waddaka cikin kudi. Babban dan kasuwar man fetur ne da gas. Yana da dukiyar da ta kai $300 million.

1.Sarki Mohammed VI

Sarki Mohammed shi ne sarkin Morocco. Ya hau karagar mulkin ne a 1999 bayan rasuwar mashahurin mai arzikin mahaifinsa. Shine basarake mafi arziki a a nahiyar Afirka kuma yana da dukiyar da ta kai $10 billion.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel