Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta tabbatar da Sule matsayin gwamnan Nasarawa

Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta tabbatar da Sule matsayin gwamnan Nasarawa

Kotun daukaka karar dake zamanta a Makurdi, jihar Benue ta tabbatar da Injiniya Abdullahi Sule na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) matsayin zababben gwamnan jihar Nasarawa a ranar Talata, 12 ga Nuwamba, 2019.

Kotun ta yi watsi da karar da jam'iyyar People Democratic Party (PDP) da dan takararta, Emmanuel David Ombugadu, suka shigar kan zaben 9 ga Maris.

Kotu ta kara da cewa ko shakka babu ta amince da hukuncin kotun zabe da ta yanke cewa lallai Abdullahi Sulene ya lashe zaben.

A wani labarin daban, Kotun daukaka kara da ke zama a Ibadan, babbar birnin jihar Oyo ta soke zaben Gwamna Seyi Makinde na jihar.

Kotun ta yanke hukunci ne a karar da Adelabu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya daukaka.

Kotun ta dage hukuncin kotun sauraron karar zabe wacce ta jaddada nasarar Makinde. Sai dai kuma, kotun ba ta kaddamar da Adelabu a matsayin wanda ya yi nasara ba.

Duk da umurnin kotun, gwamnan Seyi Makinde zai cigaba da kasancewa gwamna har sai kotun koli ta yanke hukunci na karshe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel