APC ta ce karya ne PDP ba ta yi mata zigidir ba a Zamfara

APC ta ce karya ne PDP ba ta yi mata zigidir ba a Zamfara

Jam’iyya All Progressives Congress (APC), ta bayyana cewa babu mambobinta da yawa da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Zamfara kama yadda gwamnatin jihar ta yi zargi.

Gwamna Bello Matawalle da shugabannin PDP a jihar a ranar Lahadi, 10 ga watan Nuwamba sun tarbi tarin masu sauya sheka daga APC a karamar hukumar Maradun da ke jihar.

Sai dai kuma Alhaji Lawal Liman, Shugaban APC a jihar ya fada ma manema labarai a ranar Talata, 12 ga watan Nuwamba a Gusau cewa duk abun farfaganda ne.

“Kawai farfaganda ne domin a yaudari jama’a.

“Wasu kamfanonin sadarwa sun rahoto cewa mambobin APC 21,000 sun sauya sheka zuwa PDP yayinda sauran suka bayyana cewa su 50,000 ne, ba mu san wanenne gaskiya ba, su fito su warware adadin tukuna,” in ji shi.

Liman ya zargi gwamnatin PDP a jihar da razanawa da kuma tursasa mambobin APC a jihar komawa PDP.

A cewarsa, mafi akasarin wadanda suka sauya sheka zuwa PDP a Muradun, an tursasa su ne.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: APC reshen Edo ta tsige Lawrence Okah daga matsayin sakatarenta

Idan za ku tuna a baya Legit.ng ta rahoto cewa kimanin yan jam'iyyar All Progressives Congress, APC, 21,000 sun sauya sheka zuwa babbar jam'iyyar da ke ci a jihar Zamfara, Peoples Democratic Party, PDP.

Wadannan suka sauya shekan sun samu tarba daga gwamnan jihar, Bello Matawalle, da shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Alhaji Ibrahim Mallaha, a Gusau, babbar birnin jihar ranar Lahadi. Yawancin wadanda suka sauya shekarn ya karamar hukumar Maradun ne, mahaifar gwamnan.

A taron, gwamnan ya yabawa sabbin yan PDP kan daukan wannan mataki da zai ciyar da jihar gaba. Ya yi kira ga mazauna jihar Zamfara su kasance masu bin doka kuma su guji rikice-rikice da zai iya mayar da jihar ruwa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel