An ci moriyar ganga: Matashi ya hana wata kilaki kudinta, sa’annan ya kasheta

An ci moriyar ganga: Matashi ya hana wata kilaki kudinta, sa’annan ya kasheta

Wani matashi dan shekara 28 Babatunde Damilare ya kashe wata mata dake harkar karuwanci a jahar Legas sakamakon takaddama data barke a tsakaninsu kan kudin ta da ya kekashe kasa ya ki biyanta, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyarmu ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a daren Juma’a, 8 ga watan Nuwamba a wani gidan karuwai dake layin Atan, cikin unguwar Surulere na jahar Legas inda matashin ya tafi don yin zina da wata karuwa mai suna Elochukuwu.

KU KARANTA: Shawara: Idan kana taimako, sai Allah Ya kara maka arziki, Inji Aliko Dangote

Sai dai bayan ta’asar tasu ne sai karuwar ta fahimci matashin ba shi da niyyar biyanta kudin aikinta, daga nan sai rikici ya kaure tsakaninsu, sai matashin ya zaro wuka ya caccaka ma karuwar, sa’annan ya yanke mutane biyu da suka yi kokarin kama shi.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Legas, Bala Elkana ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace: “A yayin da suke fadan ne Babatunde ya caccaka ma Elochukwu wuka a wuya, inda nan take ta fadi matacciya.

“Daga bisani tawagar jami’an Yansanda a karkashin jagorancin CSP Adebayo Adeoya sun kamo Damilare, sa’annan sun dauke gawar Elochukwu zuwa dakin ajiyan gawa na babban Asibitin Mainland domin gudanar da bincike.

“Zamu gurfanar da mutumin gaban kotu da zarar mun kammala gudanar da bincike.” Inji shi.

A wani labarin kuma, hankula sun tashi a unguwar Mahutan jahar Kaduna dake cikin karamar hukumar Igabi ta jahar, inda wasu gungun miyagun yan bindiga suka yi awon gaba da wani malamin jami’ar Ahmadu Bello dake garin Zaria, Adamu Chinoko.

Jama’a sun kara shiga halin kidimewa ne yayin da dan uwansa mai suna Umar Chinoko, wanda shi ma malami ne a kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna ya tafi ya kai musu kudin fansa kamar yadda suka bukata, amma suka sake yin garkuwa da shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel