Shehun Borno ya yi wa wani soja a fadansa sarauta

Shehun Borno ya yi wa wani soja a fadansa sarauta

- Shehun Barno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi ya nada wani sojan Najeriya sarauta

- Sojan aka tabbatarwa da sarautar 'Zanna' bai dade da samun karin girma ba a rundunar sojin Najeriya

- Shehun yayi kira ga jama'a da su ajiye banbancin addini, kabila, al'adu da siyasa don kawo cigaba a jihar Barno da kasar nan baki daya

Shehun Barno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi ya yi nadin sarauta ga sojin Najeriya a fadarsa. Sojan, Donatus Vonkong, wanda aka karawa girma zuwa Master Warrant Officer a rundunar sojin, ya samu sarautar 'Zanna' a ranar Lahadi.

"Ko kana aikinka ko kayi murabus, an amince da ka yi aikinka a matsayin Zann a fadar nan," Shehun Barno ya sanar da Donatus Vonkong jim kadan bayan nadin sarautar.

DUBA WANNAN: Wasu abubuwa 5 da jama'a basu sani ba a kan Mamman Daura

Yayin addu'ar dawwamammen zaman lafiya a Barno da sauran bangarorin kasar nan, basaraken yayi kira da ayi watsi da banbancin addinin, kabila, al'adu da siyasa don kawo zaman lafiya.

Hakazalika, ta bangare bikin murnar maulidin annabi Muhammadu SAW, Shehun ya shirya cin abincin rana a ranar Asabar a fadarsa tare da sarakan gargajiya, addinai da sauran mutanen gari.

"Wannan bikin maulidin mai albarka an kasance ana yinsa ne tun kaka da kakanninmu. Lokaci ne da dagatai, masu sarauta da 'yan jihar Barno ke haduwa don bikin tare da neman albarka da tsaron Allah a Barno," in ji shi.

Shehu Barno, wazirinsa da wasu 'yan masarautar sun jagoranci masu ziyara a babban masallacin Maiduguri wajen saukar Qur'ani da addu'o'i.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel