Tashin hankali: Uba ya yiwa dansa yankan rago bayan ya koma dan luwadi

Tashin hankali: Uba ya yiwa dansa yankan rago bayan ya koma dan luwadi

- Bayan ya gano cewa dan shi ya koma harka da 'yan luwadi, uba ya yanke shawarar yiwa dansa yankan rago

- Lamarin da ya faru a kasar Iraqi dan ya bayyana dalla-dalla yadda lamarin ya kasance

- Ya bayyana cewa kawai ya tashi daga bacci ne ya iske mahaifinsa ya dora masa wuka a makogwaro

Wani matashi mai shekaru 17 wanda aka bayyana sunan sa da Seran M ana zargin mahaifinsa da kai masa hari saboda ya koma dan luwadi. Mahaifin yayi masa wannan aika-aika ne a gidansu da ke Central-Western Swiss Canton of Bern.

Kamar yadda matashin ya bayyana, ya tashi barci ne ya samu mahaifinsa tsaye a kansa da wuka a makogwaronsa.

Mahaifin da ba a bayyana sunansa ba, ya kira dan nasa da suna dan luwadi kafin ya yanka masa makogwaro da wata kakkaifar wukar, kamar yadda rahoto ya nuna.

Seran, wanda asalin dan kasar Iraqi ne, ya sanar da kafafen yada labarai cewa: "Na kasance mai boye halayyata ta luwadi daga dangina."

Duk da ya san matsayar addininsa akan luwadi, matashin ya ce har yanzu bai ga dalilin da zaisa mahaifinsa kuma musulmi nagari zai aikata hakan ba.

Seran ya yarda cewa sa'a ce kadai ta sa ya kwaci kansa daga hannun mahaifinsa inda ya tsallake katanga ya tsere.

KU KARANTA: Shikenan ta faru ta kare: Wata daya da mutuwar mahaifiyar Nnamdi Kanu mahaifinsa shima ya ce ga garinku nan

Kafafen yada labaran kasar sun ce makwafta sun kira taimakon gaggawa inda aka kwashi Seran zuwa asibitin Jami'ar Bern sakamakon munanan raunikan da ya samu a makogwaro, kirji, baya da kuma hannayensa.

Seran ya sanar da manema labarai cewa: "Sa a daya da na samu itace, mahaifina bai yi nasarar tsinke babbar jijiyar wuyan ba amma ya raunata makogwarona, sai da aka sa ni suman wucin-gadi a asibitin."

Bayan watanni shida da aukuwar lamarin, matashin na rayuwa a wani bangare daban na Swiss Canton dake birnin Bern, wanda shine birni na biyu mafi girma a kasar.

Sakamakon munanan tabo da ke jikinsa, matashin yace suna tuna masa lamarin sosai.

Seran ya ce: "Ina ganin raunikan a madubi ko kuma idan na dau hotuna, zan kasance dasu har karshen rayuwata."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel