Da duminsa: An damke barauniyar jaririya a filin jirgin saman Aminu Kano
Jami'an Tsaron filin jirgin sama AVSEC na filin jirgin Malam Aminu Kano dake unguwar Takia jihar Kano sun samu nasarar damke wata mata ta saci jaririyar wata shida tana kokarin guduwa da ita.
Jaridar Daily Trust ta bada rahoton cewa an damke matar ne yayinda take kokarin shiga jirgin zuwa Legas a ranar Lahadi, 10 ga Nuwamba, 019.
Bayan da jami'an tsaron suka nemi jin bahasin me ya samu yarinyar da tunda suka zo take bacci, matan sun bayyana cewa sun sato yarinyar ne daga Kaduna kuma an ba ta maganin bacci ne da niyyar kai ta Legas.
Zamu kawo muku cikakken rahoton....
A wani labarin mai kama da haka, Hukumar binciken leken asiri DSS ta damke wasu masu satan kananan yara biyar kan laifin satan yara biyu a karamar hukumar Zuru ta jihar Kebbi.
A cewar DSS, daga cikin wadannan mutanen akwai wata babbar malamar asibiti a asibitin Usmanu Danfodio dake jihar Sokoto. Malamar asibitin mai suna, Helen Samuel, da abokan aikinta hudu Dorathy Okonkwo, Comfort Nwanko, da Uchenna Benedict yan jihar Anambara da Delta; sannan wani Moses dan garin Zuru a jihar Kebbi.
Wannan ya biyo bayan rahoton da aka samu daga iyayensu, Yusuf Henso da matarsa Rabi Kabiru da suka kai kara ofishin yan sanda kan bacewar yaronta, Hussaini dan shekara 1 da wata 4.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng