Daga zuwa zaman jego, siriki ya dirkawa mahaifiyar matarsa ciki

Daga zuwa zaman jego, siriki ya dirkawa mahaifiyar matarsa ciki

- Wata uwa da taje zaman jego ta dawo da tsarabar cikin da mijin 'yarta yayi mata

- Wani ma'abocin amfani da kafafen sada zumunta mai suna Uncle Chike ya bayyana yadda matar mai shekaru 57 ta samu cikin surikinta

- Ta je wa 'yarta zaman jego ne bayan da ubangiji ya albarkacesu da haihuwar diya mace

Wata uwa da taje wa ‘yarta zaman jego ta samu tsarabar ciki da mijin ‘yarta ya dirka mata.

Wani ma’abocin amfani da kafafen sada zumunta, Uncle Chike ya bayyana labarin a shafinsa. Ya bayyana yadda matar mai shekaru 57 ta samu ciki da mijin ‘yarta bayan da taje zaman jego saboda haihuwar da ‘yarta tayi.

Yace, kaji tsoron matan Fatakwal. Ta ya zaki je zaman jego ki bige da samun cikin mijin ‘yarki? Ta yaya? Akan me mata mai shekaru 57 zata samu ciki da sirikinta? Wanne irin haukar karshen duniya ce wannan?

DUBA WANNAN: Wata mata ta kashe jaririn da ta haifa a Kano

Daga nan bai cigaba da bada bayani akan labarin ba.

A kwanakin baya, Legit.ng ta ruwaito yadda wata budurwa cikin tashin hanklai ta ke neman sahawara a kafafen sada zumunta.

Budurwar ta bayyana yanda mijin yayarta ya fara saninta mace. Tace sunyi shekaru goma suna sha’aninsu da mijin yayartan. Ta tabbatar da bata taba sanin wani da namiji ba banda wannan mijin yartan. Tana da ta sanin lamarin tare da neman shawarar

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel