An damke tsohon Soja mai sayarwa yan siyasa jarirai

An damke tsohon Soja mai sayarwa yan siyasa jarirai

Jami'an sashen IRT na hukumar yan sanda karkashin DCP Abba Kyari sun damke wani tsohon Soja, Samuel Adagbo, da laifin sayarwa yan siyasan jihar Delta sabbin jarirai.

An damke Samuel Adagbo mai shekaru 73 a duniya tare da abokan aikinsa Faith Desmond, Sunday Chinedu, da Joy Monday.

Yayinda Joy Monday ta kasance mai sayarwa Samuel Adagbo jariran, Chinedu ne yayi silar sayar da yara uku, wanda Samuel Adagbo ya sayarwa wani dan siyasa mai sune Francis.

Jaridar City Round ta bayyana cewa Samuel Adagbo wanda mazaunin garin Biri ne yana da asibiti da dakin ajiye gawawwaki a jihar Delta.

DUBA NAN APC ta samu gagarumin nasara, Akpabio ya samu nasara a kotu

Adagbo yace: "Na shiga hukumar Sojin Najeriya a shekarar 1968 lokacin yakin basasa kuma na yi murabus a Mayun 1982. Ina aiki a makarantar koyar da aikin Ungozoma na hukumar.

A 1984, na yi rijistan asibitin mata mallaki na karkashin ma'aikatar lafiya. Ina da dakin ajiye gawawwaki a garin. Ban yi rijista ba amma ban san ya sabawa doka ba."

Adagbo ya bayyana cewa ya sayarwa wani dan siyasa mai suna, Francis, sabbin jarirai biyu a farashin N450,000.

Hakazalika an damkeshi da wata bindiga kuma ya bayyana cewa ya sayi bindigan N235,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel