Babu takun saka tsakanin Buhari da Osinbajo - Garba Shehu

Babu takun saka tsakanin Buhari da Osinbajo - Garba Shehu

Bayan kimanin watanni uku ana rade-radin cewa akwai takin saka tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osinbajo, mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana gaskiyar maganar.

Ya karyata dukkan rahotannin cewa abubuwan da ke faruwa na ragewa mataimakin shugaban kasar aiki kokarin rage matsayin ofishinsa ne.

Garba Shehu yace: "Fadar shugaban kasa na son karyata dukkan rahotannin cewa akwai rikici tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osinbajo."

"Rahotannin kafafen yada labarai da aka samu daga bakunan wasu yan adawa dake suka lashi takobin daukan labarai daga fadar shugaban kasa domin tayar da hankalin al'umma."

"Alakar da ke tsakaninsu (Buhari da Osinbajo) na nan daram dam cikin yarda da aminci, zasu tabbatar da cigabar rana goben kasar nan."

"Ba'a rage ma'aikata domin cin mutunci ko rage matsayin ofishin mataimakin shugaban kasa ba, kamar yadda wasu yan fadar shugaban kasa ke nunawa."

"Buhari ke juya mulkinsa. Kafafen yada labarai su daina baiwa wani ikon shugaban kasa. Babu wanda yafi karfin Buhari ya juyashi."

Legit.ng ta kawo muku fikafiki biyar da Buhari ya figewa Osinbajo cikin yan kwanaki da suka gabata.

1. Rusa kwamitin tattalin arziki dake karkashin Osinbajo da nada sabuwa wacce ba shi a ciki

A ranar 16 ga Satumba, shugaba Buhari ya rusa kwamitin farfado da tattalin arziki da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, ke jagoranta kuma ya nada sabuwar kwamitin masu bashi shawara kan tattalin arzikin karkashin Farfesa Doyin Salami.

2. Sai Osinbajo ya nemi umurnin Buhari kafin ya aikata komai

A ranar 17 ga Satumba, shugaba Buhari ya bada umurnin cewa sai mataimakinsa ya nemi umurnin Buhari kafin wanzar da wani abu kan ma'aikatun da karkashin ofishin mataimakin shugaban kasa.

Haka ya sabawa yadda suka fara gudanar da mulki inda Osinbajo na da daman aiwatar da abubuwa ba tare da sanar da Buhari ba.

DUBA NAN: Babu wanda yafi karfin Buhari ya juya shi - Garba Shehu ya tabbatar da koran hadiman Osinbajo

3. Dauke shirye-shiryen jin dadin al'umma daga karkashinsa zuwa sabuwar ma'aikata

A ranar 1 ga Oktoba, Buhari ya dauke shirin jin dadin al'umma na N-Power, Trader Moni, Market Moni, ciyar da yan makaranta da sauransu daga ofishin mataimakin shugaban kasa zuwa sabuwar ma'aikatar tallafi, jin dadin al'umma da manajin annoba karkashin Hajiya Sadia Umar Farouq.

4. Rattaba hannun Buhari kan dokar harajin mai a Ingila

Sabanin yadda Buhari ya ke yi a baya idan ya tafi Landan na mika ragamar mulki ga Osinbajo, wannan karon Buhari yana mulkan Najeriya daga Ingila. Abin ya kai sai dai Abba Kyari ya kai masa dokar karin kudn harajin hakar mai a ruwa Ingile ya rattaba hannu.

5. Sallamar hadiman Osinbajo 35

A ranar Laraba, rahotannin sun fara bayyana cewa shugaban kasa ya sallami hadiman Osinbajo 35 ba tare da wani laifi da suka aikata ba. Legit.ng ta tabbatar da hakan daga bakin hadimin Buhari kan NSIP, Ismail Ahmad.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel