Masu garkuwa da mutane sun aike wa wani dan majalisa wasika ta barazana

Masu garkuwa da mutane sun aike wa wani dan majalisa wasika ta barazana

Mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar jihar Kaduna, Shehu Yunusa Pambeguwa, ya yi magana aka abinda ya kira da rashin isasshen tsaro a majalisar jihar da gidajensu sakamakon wasikar barazanar da ta iso masa daga masu garkuwa da mutane.

Dan majalisar, wanda shine mataimakin shugaban kwamitin majalisar akan tsaro da bayanan sirri, ya tada zancen ne yayin da kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya bayyana gaban majalisar don kare kasafin kudin 2020 na ma'aikatarsa.

Dan majalisar ya bukaci 'yan sanda da su dinga tsaron gidansa bayan barazanar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Buhari na iya neman zarcewa kan mulki karo na uku - Buba Galadima

Ya kwatanta tsaron da ke majalisar da 'rariya' wacce 'yan daba zasu iya kutse cikin farfajiyar.

Dan majalisar ya kara da yin bayani akan daya daga cikin 'yan majalisar da aka sace.

"Duk da an saceshi ne akan hanya, amma ko a cikin gidajenmu muna samun barazana. Akwai lokacin da na bukaci 'yan sanda da su koma gadin gidana saboda iyalaina," in ji shi.

Ya bukaci kwamishinan tsaron cikin gida da yayi wani abu akan samun cikakken tsaron 'yan majalisar.

A maida martaninsa, Samuel Aruwan ya roki 'yan majalisar da su kara hakuri saboda akwai abinda ba zai iya fada ba saboda 'yan jaridu.

Ya roki 'yan majalisar da su shirya taron tsakaninshi dasu wanda zai bayyana musu kokarin da gwamnati ke yi don habaka tsaro a jihar.

Ya kara da cewa, gwamnati zata Rana ababen hawa 80 ga Operation Yaki a matsayin hanyar habaka da inganta tsaro a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel