N140,000 na siya yaran 2 - Mijin matar aka damke a tasha tana kokarin guduwa Onitsha da yara Hausawa
Kakakin hukumar yan sandan jihar Legas, Bala Elkana ya bayyana cewa matar da aka damke da mijinta suna kokarin tafiya da wasu yara biyu garin Onitsha siya sukayi.
Mutumin mai suna Chukwunoso Happiness ya shiga hannun hukumar kan laifin safarar kananan yara.
Dan sandan ya bayyana cewa mijin da matarsa sun sayi yaran a farashin N140,000.
A cewar matar, ta sayi yaran ne daga wani gidan marayu dake Jos, jihar Pleateau wajen wata mata mai suna Mama Oyoo.
Mun kawo muku rahoton cewa hukumar yan sanda a jihar Legas ta tabbatar da damke wata mata da ta sace yara maza biyu a watan jihar Arewa a tashar motar zuwa Onitsha, jihar Anambara, kudancin Najeriya.
A damke ta ne a tashar Chemist Bus Stop dake kusa da kasuwar Alaba a jihar Legas. Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Bala Elkana, ya ce matar da mijinya a yanzu na hannun hukumar yan sanda.
Malam Abba Abdullahi wada idon shaida ne ya yi bayan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito cewa wani dattijo ne ya ga matar tare da yara biyu a tasha suna kokarin shiga motar bas zuwa Onitsha.
Yace: "Dattijon ya ji yaran suna Hausa, sai ya kira Sarkin Hausawan yankin wanda ke kusa da unguwar Alaba Rago."
Da Sarkin Hasusawan ya samu labarin, sai ya aika jami'an tsaro da fadawansa wajen kuma aka damketa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng