Hukuncin kotun koli: Jigon APC Okechukwu ya yaba ma Atiku, ya taya Buhari murna

Hukuncin kotun koli: Jigon APC Okechukwu ya yaba ma Atiku, ya taya Buhari murna

Osita Okechukwu, Wani jihar jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya yi kotafin cewa dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya rasa damarsa a zama Shugaban kasa a 2003.

A wannan shekarar ne aka tattaro cewa Atiku, a matsayin mataimakin shugaban kasa ya bugar da farin jininsa da ikonsa ga tazarcen Olusegun Obasanjo.

A cewar Okechukwu, wanda ke jagorantar muryar Najeriya (VON) a matsayin darakta-janar, Atiku ya cancanci yabo akan kalubalantar kayen da ya sha a hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kotu.

Okechukwu, wanda ya taya Buhari murnar nasarar da ya samu a kotun koli a wani jawabi a Abuja a ranar Alhamis, 31 ga watan Oktoba, ya ce tunda ya rasa damarsa a 2003, 2019 bata kasance sa’ar Atiku ba.

KU KARANTA KUMA: Kotun daukaka kara ta soke sallamar dan majalisan PDP a Osun

"Atiku ya rasa damarsa na zama shugaban kasa a 2003 lokacin da sama da gwamnoni 20 da manya da dama ke bayansa. ya fada tarkon shugaban kasa Obasanjo sannan ya rasa shugabanci," Okechuwu ya yi zargi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel