Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta kwace kujerar dan majalisar APC a Kano

Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta kwace kujerar dan majalisar APC a Kano

- Kotun daukaka kara ta kwace kujerar dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru da Bebeji a tarayya

- Kotun ta yanke hukuncin cewa, sakamakon zaben na karshe da aka cike Form EC(8)E dashi ba sahihi bane

- A don haka ta kwace kujerar tare da umartar a yi sabon zabe a kananan hukumomin biyu

A ranar Juma'a ne kotun daukaka kara ta soke zaben dan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru/Bebeji a majalisar dattawa kuma ta bada umarnin yin sabon zabe, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Kotun daukaka karar ta soke dukkan zaben da aka yi a kananan hukumomin biyu sakamakon ganowa da tayi cewa sakamakon zaben na karshe da aka cike Fom EC(8)E lalatacce ne.

DUBA WANNAN: Shari'ar Buhari da Atiku: Tambuwal ya yi tsokaci kan hukuncin da kotun koli ta yanke

Mai shari'a Adedotun Adfoke-Okoji yayin yanke hukuncin ya ce, tunda an lalata sakamakon, babu yadda za a yi a gano asalinsa.

Idan zamu tuna, a ranar 13 ga watan Satumba, kotun sauraron kararrakin zabe ta tabbatar da Nasarar Jibrin na jam'iyyar APC a matsayin dan majalisa mai wakiltar Bebeji da kiru na jihar Kano a tarayya.

A hukuncin kotun, wanda ya samu jagorancin Jastis Nayai Aganaba, ya kori karar Aliyu Datti Yako da kuma PDP da ke kalubalantar nasarar Jibrin.

Kotun sauraron kararrakin zaben ta yanke cewa, masu karar sun kasa bayyana shaidu akan zargin da suke wa wadanda sukayi kara.

Yako da jam'iyyarsa ta PDP sun ja Jibrin, jam'iyyar APC da hukumar INEC gaban kotun zabe ne saboda rashin gamsuwa da sakamakon zaben da kuma zargin magudi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel