Kisan shugaban ISIS: Matarshi ce ta fadawa Amurka inda yake boye

Kisan shugaban ISIS: Matarshi ce ta fadawa Amurka inda yake boye

Rahotanni kan yadda aka samu labarin inda marigayi shugaban kungiyar ISIS, Abubakr AlBaghdadi, yake buya ya bayyana.

Jaridar New York Daily Report ta bayyana cewa daya daga cikin matan Al Baghdadi ce ta bayyanawa Sojojin Amurka inda mijinta yake.

An damke matar ne a kasar Iraqi makon da ya gabata tare da wani mutumi wanda ke taya kungiyar ISIS safarar kaya.

A cewar jaridar, matar ta bayyanawa Amurka cewa mijinta na wani kauyen Barisha a Arewacin Syriya.

KU KARANTA: Yadda shari'ar kotun koli tsakanin Buhari da Atiku ke gudana

A ranar Lahadi, shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa shugaban kungiyar mayakan ISIS, Abubakr Baghadadi, ya mutu a wani harin da jami'an sojin Amurka suka kai masa a Arewa maso yammaci Siriya.

Trump ya bayyanawa duniya cewa sojojin sun hallaka mayakan ISIS da dama inda suka zo gab da damke Al-Bagadadi, kawai sai ya tayar da Bam ya kashe kansa.

Trump yace; "Ya tayar da rigar bam, ya kashe kansa"

"Ya mutu bayan kaiwa karshen rami na da yake buya yana kuka."

Trump ya ce an kai masa harin ne tare da gudunmuwar kasar Rasha, Syriya, Turkiyya da Iraqi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel