Assha: Sarki ya sallami fadawarsa biyu da aka kama suna aikata zina

Assha: Sarki ya sallami fadawarsa biyu da aka kama suna aikata zina

Sarkin kasar Thailand ya sallami fadawarsa guda hudu, biyu daga cikinsu saboda laifin aikata zina a wata yunkuri da ake yi na tsaftace fadar da aka dauki mako guda ana yi.

Sarkin Thai Maha Vajiralongkorn, mai shekaru 67 ya bayar da umurnin a kori fadawarsa maza biyu daga sashin 'kula da cikin gida', kamar yadda Royal Gazette ta sanar a ranar Talata.

Sanarwar ta ce, "sun aikata munanan ayyuka da kuma zina".

Sauran fadawar biyu da aka kora sun gaza cika ka'idojin da ake bukata kafin zama bafade hakan ya sa aka sallame su ba tare da wani allawus ba a cewar gazette.

DUBA WANNAN: A wajen kananan yara nake samun gamsuwa, in ji wani dan luwadi

Akwai dokar kasar da aka kafa don kare mutunci da kimar gidan sarautar na Thailand hakan yasa ba zai yi wu a gudanar da wani binciken kwaf-kwaf ba kan wani mataki da sarkin ya dauka a kasar.

Wannan tankade da rairaiyar da aka yi a fadar yana zuwa ne bayan an kwace wa sa-dakar sarkin, Sineenat Wongvajiraoakdi dukkan mukamanta watanni uku bayan nadin da aka yi mata.

An zarge ta da rashin da'a da kuma 'saba wata umurni, na Sarauniya Suthida.

Sarki Vajiralongkorn ya auri matarsa ta hudu, Suthida a watannin farkon wannan shekarar.

Tsohuwar sa-dakar sarkin, Sineenat ta kauracewa idon al'umma tun bayan korar ta da aka yi daga fadar.

Bayan korar ta, an kuma sallami wasu fadawa shida kan wasu abubuwa da aka kira 'munannan ayyuka'.

Sarki Vajiralongkorn ya dare kan karagar mulki a 2016 bayan rasuwar mahaifinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel