Karshen duniya: Yarinya 'yar shekara 9 ta rubutawa yaro dan shekara 9 wasikar soyayya

Karshen duniya: Yarinya 'yar shekara 9 ta rubutawa yaro dan shekara 9 wasikar soyayya

- Wata mata ta bayyana irin halin da ta shiga bayan wata yarinya 'yar shekara 9 ta rubutowa danta dan shekara 9 wasikar soyayya

- Yarinyar dai ta rubuto wasikar ne domin taji matsayinta a wajen yaron, inda take tambayar shi hakan a cikin wasikar

Wata mai suna Birddie-T ta wallafa wani labari a shafinta na Twitter, inda ta bayyana yadda wata yarinya 'yar shekara 9 ta rubutawa danta mai shekara 9 wasikar soyayyar, Birddie ta roki mutane su taya ta jimamin wannan wasika.

A cewar ta yarinyar ta nuna tana son dan nata sosai kuma za ta yi ko menene domin ta tabbatar da soyayyarta a wajen shi.

Sai dai kuma ana haka ashe akwai wata yarinya ita ma mai suna Lethabo wacce ita ma take son yaron, to ita Lwandle ta rubuta wasikar ne domin ta san matsayinta a wajen shi.

A cikin wasikar, a lokacin da Lwandle take bayyana soyayayar ta a gareshi ta bayyana cewa Lethabo ba ta iya soyayya ba, saboda haka ita ce wacce za ta iya kula da shi yadda ya kamata.

Mahaifiyar yaron ta wallafa wannan wasika da aka rubutawa dan na ta a shafin ta na Twitter, ga dai abinda yarinyar ta rubuto:

KU KARANTA: Bidiyo: Yadda sojoji suka sanya wani barawo ya kamo kifin oga a cikin kwata bayan ya saci takalmi

"Ya kai Koketso daga Lwandle

"Kayi hakuri na sake rubuto maka wata wasikar. Na rubuto wannan wasikar ne saboda ina so na tambayeka wani abu, kuma dan Allah ka fada mini gaskiya. Shin ni kake so ko Lethabo ko Bonelo. Abinda zan gaya maka yana da rikitarwa. Lethabo har yanzu tana sonka. To tambayar tawa a nan shine shin kai ma har yanzu kana sonta ne?

"Idan har kana sonta babu matsala, kuma soyayyar dana ke yi maka ne yasa na rubuto maka wannan wasikar. Ina fatan har yanzu akwai soyayya ta a zuciyarka. Lethabo ba ta da matsala da kai a yanzu, duk da dai ta damu da kai amma ba a matsayin masoyi ba. Da tana soyayya da Kelvin ne bayan sun rabu kuma yanzu ta dawo take sonka.

"Ta tilasta ni na rabu da kai saboda ita tayi soyayya da kai. Dan Allah kada kowa ya san da wannan maganar ta mu har ita kanta Lethabo. Ina sonka."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel