Bidiyo: Budurwa ta tumurmusa saurayinta a kasa bayan ta kama shi yana lalata da wata

Bidiyo: Budurwa ta tumurmusa saurayinta a kasa bayan ta kama shi yana lalata da wata

- Wani bidiyo dake ta yawo a shafukan sadarwa ya bayyana yadda wata budurwa ta dinga dukan saurayin ta bayan ta kama shi yana lalata da wata

- Budurwar wacce take yaren Fante na kasar Ghana, an jiyo tana cewa budurwar da ya kwanta da ita din karuwa ce

- Lamari na cin amana a wajen masoya dai ya zama tamkar ruwan dare a wannan lokacin, yayin da kowanne a cikin masoyan idan ya samu dama yana boyewa ya ci amanar dan uwanshi ne

Kamar yadda kowa ya sani cin amana ya riga yayi katutu a cikin jinin mutane yake, yanzu haka lamarin ya zama tamkar gaskiya yayin da yanzu kowanne lungu da sako ka shiga masoya na fuskantar matsalar cin amana wala Allah ga macen ko kuma ga namijin.

Makonni kadan da suka gabata, wata daliba a jami'ar kasar Ghana, an wallafa wani bidiyo ita da saurayinta tana zane shi da takalmi silifas, bayan ta kama shi yana lalata da wata budurwar.

Yanzu kuma wani sabon bidiyo ne na wata budurwa 'yar kabilar Fante ta yiwa saurayinta dukan tsiya, bayan shima ta kama shi yana lalata da wata budurwa wacce ta bayyana cewa karuwa ce, yanzu haka dai bidiyon ya karade ko ina a shafukan sadarwa.

KU KARANTA: Allah sarki: Tsohuwa ta dage tana faman zabga bara ga wani mutum-mutumin roba a tunanin ta mutum ne

A bidiyon an gano saurayi da budurwar a kan gado budurwar ta hau kanshi tana ta dukan shi da hannu saboda ciwon cin amanar ta da yayi da wata budurwar.

Ga dai bidiyon yadda lamarin ya kasance a kasa:

Lamari na cin amana a wajen masoya dai ya zama tamkar ruwan dare a wannan lokacin, yayin da kowanne a cikin masoyan idan ya samu dama yana boyewa ya ci amanar dan uwanshi ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel