'Yan sanda a Dubai za su yiwa karuwan Najeriya kwasar kaji bayan sun samu gawar wani Balarabe da ya mutu a yayin da yake lalata da wata karuwa

'Yan sanda a Dubai za su yiwa karuwan Najeriya kwasar kaji bayan sun samu gawar wani Balarabe da ya mutu a yayin da yake lalata da wata karuwa

- Bayan mutuwar wani Balarabe da ya kwanta da wata karuwa a kasar Dubai

- Yanzu gwamnatin kasar ta yanke shawarar kama duk wata mace mai zaman kanta da aka gani a kasar

- Bayan an kama su za a mayar da su kasashen su, dalilin wannan lamari da ya faru

Hukumar 'yan sanda ta Hadaddiyar Daular Larabawa sun gama shiri tsaf domin tarkato kan karuwai masu zaman kansu a kasar, bayan sun samu gawar wani Balarabe da ya mutu a lokacin da yake zina da wata karuwa a Otel.

Wannan lamari dai ya faru a yankin Hilly Tower Sharjah, hakan ya sanya aka sanar da 'yan sanda su kama wasu mata dake yankin da ake tunanin karuwai ne.

A wani bidiyo da aka sanya a shafukan sadarwa, jaridar Information Nigeria ta gano cewa an umarci 'yan sandan kasar da su tattaro duka mata 'yan Afirka da suke zaman kasu a kasar, bayan mutuwar wannan Balarabe.

KU KARANTA: Hotuna: Matashin saurayi mai basira ya kera sabuwar mota a Najeriya

Ga dai abinda mutumin da ya wallafa bidiyon yake cewa:

"Karuwa 'yar Najeriya ta kwanta da Balarabe ya mutu a lokacin da yake lalata da ita. Yanzu gwamnatin Dubai za su dawo da duk wata bakar mace da suka gani tana yawo akan titi.

"Lamarin ya faru jiya a yankin Hilly Tower Sharjah, abin babu dadin ji, yanzu haka an kama kusan mata 18."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel