Babbar magana: Yaki ne yake neman barkewa a jihar Kogi ba zaben gwamna ba - Matar dan takarar gwamnan jihar

Babbar magana: Yaki ne yake neman barkewa a jihar Kogi ba zaben gwamna ba - Matar dan takarar gwamnan jihar

Uwargidar wani dan takarar gwamna na APC a Kogi, Prncess Zahrah Mustapha Audu, ta yi zargin cewa yan takarar gwamna a zaben ranar 16 ga watan Nuwamba a jihar na shirn yaki ne amma ba zabe ba.

Princess Audu ta cigaba da zargin cewa akwai wani lamari dake gudana na shigo da makamai gabannin zaben, koda dai bata ambaci majiyar bayaninta ba.

Ta ce za ta kwashi iyayen yan bangan siyasa aiki a fadin dukkanin yankunan jihar domin tabbatar da ganin an gudanar da zabe ba tare da wani rikici ba.

"Dukkanin yan takarar dake neman kujerar gwamnan Kogi na nuna alamu na cewa sun shirya yin yaki ne fiye da kamfen din zaben. Idan kana kamfen din jagoratar jihar, za ka fita ne kana neman jan hankalin masu zabe, ka lallashe su sannan ka fada masu tanadin da kayi masu, amma su (yan takarar) na siyan motoci marasa jin harbi da duk wani makami da alburusai," jaridar Daily Trust ta alakanto inda take fadin hakan.

KU KARANTA KUMA: Kuna da damar sauya sheka, Sule Lamido ya fada ma mambobin PDP

Ta kuma yi kira ga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da shugaban kasa Muhammadu Buhari akan su shiga lamarin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel