Innalillahi: Masu fizgen waya sun hallaka matashi har lahira
- A ranar Litinin ne da ta gabata wasu bata-gari suka hallaka wani matashi har lahira
- Kamar yadda kanin matashin ya wallafa a shafinsa na Facebook, bata-garin sun kashe yayansa ne yayin kokarin fizge wayar hannunsa
- Shafin jekadiyar Zamfara kuwa sun wallafa cewa, watanni biyar kacal kenan da rasuwar masoyiyar Yaya Ameenu
Wasu da ake zargin bata-gari ne sun soke wani matashi da wuka inda ya mutu har lahira.
Lamarin ya auku ne a garin Jos a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba, 2019 yayin da bata-garin suka yi yunkurin fizgewa saurayin wayarsa.
KU KARANTA: Yanzu - Yanzu: An cigaba da harar 'yan Najeriya da ke kasar Afirka ta kudu
Matashin mai suna Ameenu dan asalin jihar Zamfara ne,ya rasu ne sakamakon soka mishi wuka da masu fizgen wayar suka yi.
Ga abinda kaninsa ya rubuta a shafinsa na Facebook: "Da Allah muke, gareshi zamu koma. Mun rasa Yaya ameenu a yau sakamakona kasheshi da bata-gari masu fizgen waya sukayi a garin Jos yau. Allah yas aljanna ta zamo makomarsa."
Abinda wani abokinsa ya wallafa shine: "Daga Allah muke, gareshi zamu koma. Yanzu nake jin rasuwar abokina Yaya Ameenu. Ya rasu ne a daren jiya. Rashin babu dadi kuma munsan hawaye ba zai dawo da kai ba. Abu daya dai nake da tabbaci; Ubangijin sammai zai yi maka rahama. Allah ya gafarta maka zunubanka yasa aljanna makoma."
Shafin Jekadiyar Zamfara kuwa sun wallafa cewa, saurayin ya rasu ne bayan watanni biyar da rasuwar masoyiyarsa da ake sa ran zasu angwance ba da dadewa ba. Sunyi masa fatan samun rahamar ubangiji.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng