Gwamnatin tarayya na bawa 'yan Najeriya marasa karfi 621,000 naira dubu biyar a kowanne wata - Maryam Uwais

Gwamnatin tarayya na bawa 'yan Najeriya marasa karfi 621,000 naira dubu biyar a kowanne wata - Maryam Uwais

- Mai bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara ta musamman a bangaren sadarwa da cigaba ta hanyar kasuwanci, Maryam Uwais, ta bayyana yawan mutanen da suke samun tallafin naira dubu biyar a kowanne wata

- Maryam ta ce labarin da ake yadawa na cewa mutane miliyan shida ne da dubu dari shida maganar ba haka take ba

- Ta ce a cikin mutum miliyan shidan mutane dubu dari shida da ashirin ne kawai suke amfana da wannan tallafi

Babbar mai bawa shugaban kasa shawara ta musamman, Maryam Uwais ta bayyana cewa kimanin mutane 620,947 marasa karfi suke amfana da tsarin gwamnatin tarayya na taimakon marasa galihu.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar dinnan da ta gabata, Maryam Uwais, ta ce mutane miliyan shida da dubu dari shida da aka ce suna amfana da wannan tsarin ba haka lisafin yake ba.

An bayyana cewa an jiyo Maryam Uwais tana bayyana cewa sama da mutane miliyan shida da dubu dari shida ne suke amfana da taimakon da gwamnati take yi na biyan marasa karfi naira dubu biyar a kowanne wata.

"Duk da cewa an yiwa mutane sama da miliyan shida rijista a wannan tsari na bada tallafi, amma iya mutum dubu dari shida da ashirin da daya ne suke amfana da wannan tsarin.

KU KARANTA: Kudin da ake kashewa mai laifi dake kurkuku a Amurka a kullum yafi albashin da ake bawa ma'aikacin gwamnatin Najeriya a wata - Ministan cikin gida

"Haka kuma zanyi tsokaci akan rahoton da yake yawo na cewa gwamnatin tarayya ta ware kason kudi na naira biliyan talatin na shekarar 2020, daga cikin biliyan dari biyar na tsarin N-SIP na shekarar 2016.

"A shekarar 2016 mun samu kaso 16 cikin dari, mun samu kaso 36 a shekarar 2017, sannan mun samu kaso 53 a shekarar 2018.

"Wannan tsari dai ya shafi sama da mutane miliyan sha uku, sannan kuma akwai kimanin mutane miliyan arba'in da hudu da suma tsarin zai amfana, wadanda suka hada da manoma, makiyaya da dai sauran su," in ji ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel