Wata kyakkyawar budurwa ta mutu bayan aminiyarta ta saka mata guba a abinci saboda ta samu karin girma a wajen aiki

Wata kyakkyawar budurwa ta mutu bayan aminiyarta ta saka mata guba a abinci saboda ta samu karin girma a wajen aiki

- Wata kyakkyawar budurwa son kowa kin wanda ya rasa ta mutu sanadiyyar guba da wata babbar abokiyarta ta saka mata a abinci

- Hakan ya biyo bayan karin girma da marigayiyar ta samu a wajen aiki, inda ita kuma kawarta ke hassada

- An bayyana cewa tare suke neman karin girman, inda marigayiyar ta samu nasara, hakan ya sanya ran dayar ya baci ta yanke hukuncin kawar da ita

Wannan kamar gargadi ne ake yiwa mutane na yadda za su zabi aboki, saboda a cikin jerin abubuwan da za su kashe mu a duniya dole mu saka aboki mai hassada a ciki.

Wata mata 'yar kasar Congo ta mutu saboda hassadar wata kawarta, hakan ya biyo bayan karin girma da aka yi mata a wajen aiki.

Kamar yadda rahoto ya bayyana kyakkyawar budurwar ta mutu ne bayan, aminiyartan ta sanya mata guba a cikin abinci.

Duka su biyun suna neman karin girma ne a wajen aikin, sai ita marigayiyar ta samu nasara akan kawarta, hakan yasa hassada ta shiga zuciyar ta inda ta yanke hukuncin daukar rayuwarta.

KU KARANTA: A doke ka a hanaka kuka: Bayan taje Fasto ya dirka mata cikin shege, matar ta zo tana rokar mijinta ya kula da jaririn

An bayyana cewa ta sanya mata guba a cikin abinci ne, inda ta bata abincin taci, cinyewa keda wuya ta ce ga garinku nan.

Yanzu haka dai an kama matar da laifin kisan kai, sai dai kuma ta musanta zargin da ake yi mata.

Yayin da ita kuma marigayiyar aka binne ta a makwanci. Wannan abin takaici ne, kyakkyawar budurwa irinta ta mutu sanadiyyar hassada da wata ke yi mata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel