Gidan Mari: Fursunonin sun kwashe tsawon shekara 8 a daure da sarkoki – Kwamishinar Kaduna

Gidan Mari: Fursunonin sun kwashe tsawon shekara 8 a daure da sarkoki – Kwamishinar Kaduna

Kwamishinar jihar Kaduna kan harkokin bil adama da cigaban jama'a, Hafsat Baba ta bayyana cewa wasu daga cikin fursunonin da aka saka na cibiyar horar da dalibai sun kasance daure cikin mari tsawon shekara takwas.

Ta kuma bayyana cewa sai da aka kira masu aikin narkar da karafuna domin su cire sarkokin daga kafafuwan fursunonin da aka ceto daga cibiyar wanda ke a Kanar Gurguwa a kaamar hukumar Igabi na jihar.

"Sun kasance a karkashin azaba. Dukkaninsu a daure suke da sarkoki. Mun kira wani mai aiki kira karafuna domin ya cire sarkokin daga kafafuwansu. Wasu daga cikinsu sun kasance a daure tsawon shekara takwas.Da ranan nan aka cire sarkokin," inji Hafsat.

Ku tuna cewa mata 22, yan kasashen waje hudu da mammalakin cibiyar horon wanda aka fi sani da Malam Niga ne aka kama bayann yan sanda sun kai samame cibiyar sannan suka ceto fursunoni 147 a ranar Asabar, 19 ga watan Oktoba.

KU KARANTA KUMA: Matasan Neja sun yi ga-zanga akan tabarbarewar hanyoyi, sun rufe babban hanyar Minna-Suleja

Hafsat ta kara da cewa an tura wasu daga cikin fursunonin dake fama da tabin hankali zua asibitin mahaukata da ke jihar domin samun kulawar likitoci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel