Yanzu-yanzu: Jirgin Buhari ya tashi zuwa Rasha (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Jirgin Buhari ya tashi zuwa Rasha (Hotuna)

Jirgin shugaba Muhammadu Buhari ya tashi daga babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja zuwa birnin Sochi, kasar Rasha domin halartan taron hadin gwiwar nahiyar Afrika da kasar Rasha.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana a jawabin da ya saki, za'a gudanar da wannan taro ne tsakanin ranar 23 da 25 ga Oktoba, kuma za'a tattauna kan fadada hanyoyin samar da tsaro, kasuwanci da hannun jari, kimiya da fasaha da arzikin iskar gas.

Shugaba Buhari ya tafi da gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, Bello Matawalle na jihar Zamfara da Kayode Fayemi na jihar Ekiti.

Hakazalika, akwai ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama; ministan hannun jari, Adeniyi Adebayi; ministan ma'adinai, Olamilekan Adegbite da ministan man fetur, Temipre Sylva.

Yanzu-yanzu: Jirgin Buhari ya tashi zuwa Rasha (Hotuna)
Yanzu-yanzu: Jirgin Buhari ya tashi zuwa Rasha (Hotuna)
Asali: Facebook

Jawabin yace: "A taron, shugaba Buhari zai gana da shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin domin karfafa alaka kan tsaro, kasuwanci da hannun jari, arzikin iskar gas."

Legit.ng ta fahimici cewa wasu shugabannin kasashen Afrika zasu halarci taron.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel