Hukumar NCC ta amince da yunkurin Airtel na datse cibiyar sadarwar Globacom saboda bashi

Hukumar NCC ta amince da yunkurin Airtel na datse cibiyar sadarwar Globacom saboda bashi

Ma'aikatar sadarwa ta tarayya wato NCC ta ba kamfanin sadarwa na Airtel izinin datse kamfanin Globacom daga kan cibiyar sadarwarta.

Hukumar kula da tsarin sadarwar tace izinin ya kasance ne saboda kamfanin Globacom ta gaza biyan bashin da ake binta na hade-haden layuka.

Wannan datsewar da za a yi zai hana masu amfani da layin Glo kiran masu amfani da Airtel. Sai dai kuma, su suna iya amsa kira daga wannan layin.

Cikakken bayani kan hukuncin ya nuna cewa matakin datsewar zai fara aiki ne daga ranar 28 ga watan Oktoba.

A farkon shekarar nan, MTN ta zargi kamfanin Globacom da rashin biyan bashin da ake binta na hade-haden layuka sannan tayi barazanar datse masu amfani da layukan Glo, wannan yayi sanadiyar da said a hukumar NCC ta shiga lamarin.

A wani jawabi mai dauke da kwanan wata 18 ga watan Oktoba, Daraktan hulda da jama’a na hukumar NCC, Henry Nkemadu, ya bayyana cewa an sanar da kamfanin Glomobile halin da ake ciki sannan an bata dammar yin sharhi kan lamarin.

KU KARANTA KUMA: Kuma dai: Yan bindiga sun yi garkuwa da wata mata da danta a garin Abuja

NCC ta bayyana cewa bayan kwanaki 10 daga ranar da aka sanar da kamfanin, masu amfani da layukan Globacom ba za su iya kira zuwa layin Airtel ba. Amma za su iya amsa kira.

Hukumar ta bayyana cewa datsewar zai cigaba da tasiri har zuwa lokacin da hukumar za ta san abun yi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel