Da sauran rina a kaba, Zakin da ya kwace a Kano ya sake cin Jimina daya (Bidiyo)

Da sauran rina a kaba, Zakin da ya kwace a Kano ya sake cin Jimina daya (Bidiyo)

Ma'aikatan gidan Zoo na jihar Kano sun bayyana cewa idan hanyoyin da ake bi na damke Zakin da ya kwace ranar Asabar ya gagara, za'a harbe dabban domin kare rayukan jama'a. Daily Nigerian ta ruwaito.

Mun kawo muku rahoton cewa Zakin ya fasa cikin gidan Jimina kuma ya lashe daya kafin jami'an gidan suka turashi cikin kejin akuyoyi kuma hallaka biyu.

Diraktan gidan Zoo na Kano, Saidu Gwadabe, ya bayyanawa manema labarai a daren Lahadi cewa har yanzu ana cigaba da kokarin cewa na kama Zakin da ransa.

Gwadade yace kawo yanzu, Zakin ya kashe Jimina biyu da akuyoyi da dama: "Zakin ya kwace gidan Jiminan kuma ya cinye biyu," a cewarsa.

Ya kara da cewa a gayyato masana kiwon dabbobin gidan Zoo na kasa sun dira Abuja domin bada gudunmuwarsa wajen kama dabban da ya kwace.

Ya ce har harbeshi da alluran kashe karfin jiki 10ml bayan ya shanye 1.5m kuma ba tayi masa tasiri ba.

Kalli biyoyin Zakin da ya kwace:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel