Bayan ta dauki kafa tun daga garinsu ta tafi wani gari domin ta hadu da saurayin da take Chatting da shi, a karshe ta gano cewa yarone dan shekara 12

Bayan ta dauki kafa tun daga garinsu ta tafi wani gari domin ta hadu da saurayin da take Chatting da shi, a karshe ta gano cewa yarone dan shekara 12

- Wani labari da wata budurwa 'yar Najeriya ta wallafa ya sanya mutane kace - nace

- Budurwar ta bayyana yadda ta tashi tun daga jihar Cross River ta nufi jihar Enugu domin haduwa da saurayinta

- Sai dai kuma kash, da zuwanta ta gano cewa mutumin da take hira da shi ba saurayi bane yaro ne dan shekara 12

Budurar ta bayyana yadda ta tashi tun daga jiharsu ta tafi wata jihar domin ta hadu da saurayin da suke hira da shi a shafin sada zumunta, a karshe ta gano cewa ba saurayi bane yaro ne karami dan shekara 12.

Budurwar wacce ta sanya sunanta a shafin sada zumunta na Twitter da @Nodobyvexx ta bayyana yadda ta tashi tun daga garin Calabar jihar Cross River ta tafi har jihar Enugu domin ta hadu da saurayin da take chattin da shi a shafin sada zumunta.

Budurwar ta bayyana cewa bayan zuwanta jihar Enugun ta gano cewa ashe da yaro dan shekara 12 take magana duk wannan lokacin.

KU KARANTA: 'Yan kai gawa sun ranta ana kare bayan kammala binne gawa sunji tana magana daga cikin kabari

Budurwar ta ce: "Kawai na kashe kudin mota a banza na tashi tun daga Calabar naje Enugu domin na hadu da saurayin da nake hira da shi sai na gano ashe yaro ne dan shekara 12."

Wannan labari da ta wallafa yasa mutane suka yi ta kace nace dangane da maganar, wasu sun bayyana cewa ai bata san cewa yaro ne dan shekara 12 ba shine yasa taje, wasu kuma sunce yaro ne dan shekara 12 amma mai kamar manya.

Wasu kuma sun bayyana cewa budurwar ma karya kawai ta shararawa mutane, kawai dai tana so ta jawo hankalin mutane ne kanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel