Ministan Buhari ya nemi taimako daga Bollywood

Ministan Buhari ya nemi taimako daga Bollywood

- Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya yi kira ga gwamnatin kasar India da ta tallafawa masana'antar fim ta Najeriya don samun karin habaka

- Mohammed ya kara da neman tallafin kasar India wajen horar da malaman tsangayar fina-finai da ke Jos

- Babban kwamishinan kasar India, Abhay Thakur, ya ce, kawancen kasar India da Najeriya har ta fannin kasuwanci, yada labarai da al'adu ne

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya hori gwamnatin kasar India dasu tallafi masana'antar fim din Najeriya da fasahohin da zasu habaka nagartar fina-finan da aka a kasar nan.

Kamar yadda Segun Adeyemi, hadimin shugaban kasa mai aiki a karkashin ministan, ya ce, Mohammed ya yi wannan kiran ne a Abuja a ranar Juma'a lokacin da ya karbi babban kwamishinan India a Najeriya, Abhay Thakur, a ziyarar da ya kaiwa ofishin ministan.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Hukumar EFCC ta cafke tsohon gwamnan jihar Zamfara

"A tunanina, masana'antar Bollywood ita ce masana'antar film mafi girma a duniya. Duk da muna alfahari da masana'antar Nollywood, a tunanina akwai bukatar bunkasa masana'antar ta fannin fasaha,"

"Ina tunanin zan maida hankali a wannan bangaren wajen ganin habakar masana'antar tare da hada alaka mai kyau tsakaninmu da kasar," in ji shi.

Mohammed ya kara da horar India da tallafa wajen kara horar da malaman tsangayar fina-finai da ke Jos don basu damar kaiwa wani matakin ilimi wanda zai karar gogar da dalibansu.

Ministan ya ce, duk da yawan mutanen da ke kasar India, akwai kamanceceniya tsakanin kasar da Najeriya, ballantana a fannin yawan al'adu da addinai.

A jawabin babban kwamishinan ga Najeriya, Thakur, ya ce, don ganin kara dankon ma'amala tsakanin kasashen biyu, ministan harkokin waje na India na shirya ziyarar manema labarai ga wasu 'yan jaridun Najeriya zuwa kasar India don gogar dasu akan al'adun Afirka da ke a kasar India.

Ya kara da mika goron gayyatarsa ga kungiyoyin al'adun don taka rawar gani a bikin al'adun India da Afirka da ke gabatowa a watan Disamba.

Babban kwamishinan, ya bayyana cewa, kasar su na jin dadin alakar kasuwanci, yada labarai da al'adu da kasar Najeriya.

Yace, akwai sama da 'yan kasar India 50,000 da ke zama a halin yanzu a kasar Najeriya, wacce ya kwatanta da babbar kawar India a fannin kasuwanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel