Masu yawan shan shayi sun lafiyan kwakwalwa - Binciken jami'ar Singapore

Masu yawan shan shayi sun lafiyan kwakwalwa - Binciken jami'ar Singapore

Masu shan shayi akai-akai sun fi lafiyan kwakwalwa - hakan yana nuna sun fi lafiyar rayuwa - fiye da maras shan shayi, sabon binciken kasar Singapore ya bayyana.

Farfesa Feng Lei, kwararren malamin lafiyar kwakwalwa a tsangayar ilimin magani na Yong Loo dake jami'ar kasa ta Singapore ya bayyana cewa shan shayi na da muhimmanci ga lafiyar kwakwalwa.

Hakazalika ya bada shawaran cewa shan shayi akai-akai na hana mutuwan kwakwalwa sakamakon tsufa.

A cewarsa: "Sakamakon binciken da muka samu hujja ne na farko da ke nuna gudunmuwar da shan shayi ke baiwa kwakwalwa. Kuma hakan na nuna cewa sha shayi sosai na rage rikicewar da yawan shekaru ke kawowa."

Bincike a baya ya nuna cewa shan shayi na da muhimmanci ga lafiyar dan Adam, kuma amfanin ya kunshi kare cutar zuciya.

Kana, binciken 2017 da Feng Lei ya nuna cewa shan shayi kullum na rage rikicewa da tsufa ke janyowa da kashi 50%.

KU KARANTA: Manoma sun fi kowa yin jima'i - Binciken kasar Ingila

A wani labarin daban, Mutum daya cikin kowani mutane bakwai masu shekarun 15 zuwa 64 a Najeriya na amfani kwaya akalla guda daya, a cewar shugaban kwamitin yaki da ta'amuni da muggan kwayoyi a Najeriya, Janar Buba Marwa.

Hakan ya banbanta da binciken masu ta'amuni na duniya da aka samu cewa kowani mutum daya cikin mutane ashirin na ta'amuni na kwayoyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel