Wannan abin kunya da yawa yake: Uba na kiran samarin 'ya'yansa ya sanya suyi zina da su shi kuma yana gefe yana kallo

Wannan abin kunya da yawa yake: Uba na kiran samarin 'ya'yansa ya sanya suyi zina da su shi kuma yana gefe yana kallo

- Wani mutumi ya aikata abin kunya, yayin da ya yiwa daya daga cikin 'yarsa cikin shege

- Mutumin dai ya bayyana cewa yana yin wannan abu nashi ne saboda ya koyawa 'ya'yan nasa yadda ake kwanciya da namiji

- Sannan kuma an bayyana cewa mutumin yana kiran samarin 'ya'yan nasa ya sanya su suyi zina da su shi kuma yana gefe yana kallo

An kama wani mutumi dan kasar Birtaniya da laifin fyade har sau 36, bayan wani bincike ya bayyana cewa yana da yara guda shida da daya daga cikin 'ya'yanshi mata.

Mutumin wanda ba a bayyana sunanshi ba, ya yiwa 'ya'yansa mata guda biyu fyade, ciki kuwa hadda wata budurwa da daya daga cikin yarsa ta haifa masa sanadiyyar lalatar da yake yi da su.

Da aka gurfanar da mutumin a gaban kotu ya bayyana cewa yana so ya koyawa 'ya'yan nasa yadda ake kwanciya da maza ne, saboda su koya kafin su fara kwanciya da samarin su.

Haka kuma an bayyana cewa mutumin ya sanya daya daga cikin samarin 'ya'yan nasa yayi zina da ita shi kuma yana gefe yana kallo, a cewar jaridar WalesOnline.

KU KARANTA: Babbar magana: Babu ni ba talaka a rayuwata, hanyar sa daban tawa daban - Jaruma Nikki

Wanda ya gurfanar da mutumin ya bayyanawa kotu cewa: "Mutumin wanda ya kamata ace ya kula da tarbiyar 'ya'yan nasa, shi ne kuma yake amfani da su yana yin zina da su saboda kawai wata bukata ta kansa."

"Na shafe sama da shekara arba'in ina aiki a matsayin alkali, amma wannan ita ce kara ta uku dana taba ji wacce ta tada mini hankali," in ji alkalin kotun Paul Thomas.

Sai dai kuma mutumin ya musanta zargi 36 da ake yi masa.

Sai dai jaridar WalesOnline ta bayyana cewa za a yanke masa hukunci a ranar Juma'ar mai zuwa.

"Kada kayi mamaki idan kaji an yanke maka hukunci mai tsawo a gidan yari," in ji alkalin kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel