Hukumar ICPC ta raba manyan motocin aikin gona ga kananan hukumomin Bauchi 6 bayan ta kwace daga hannun tsohon sanatan yankinsu dan PDP

Hukumar ICPC ta raba manyan motocin aikin gona ga kananan hukumomin Bauchi 6 bayan ta kwace daga hannun tsohon sanatan yankinsu dan PDP

Hukumar yaki da rashawa ta ICPC, ta mika taraktocin da ta karba daga sanatan jihar Bauchi.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, taraktocin na daga cikin aiyukan 2015 da mazabarsa zasu amfana dasu a karkashin SDG kuma sanata Isa Hamman Misau ya dau nauyi.

Anyi niyyar rabawa kananan hukumomin Ganjuwa, Misau, Dambam, Darazo, Aarji da Ningi ne a mazabar tsakiya ta jihar Bauchin.

Kungiyar bin diddigin aiyukan mazabu ce ta samo taraktocin a ranar 31 ga watan Yuli, 2019.

A yayin tattaunawa da manema labarai, jim kadan bayan mikasu ga kananan hukumomin 6 a ranar Laraba, Kwamishinan ICPC na jihar Bauchi, Abubakar Dutsinma, ya ce, raba taraktocin ga kananan hukumomin ya biyo bayan umarnin shugaban hukumar, Farfesa Bolaji Owosanoye.

DUBA WANNAN: Badakala: EFCC ta gabatar da karin shaidu a kan wasu tsofin gwamnonin PDP biyu daga arewa

Ya ce, an kirkiro kungiyar bin diddigin aiyukan mazabun ne tare da hadin guiwar CSO da kuma ofishin hukumar dake jihohi 12 a kasar nan.

Dustinma ya ce, "A Bauchi, kungiyar ta yi kokari wajen bibiyar aiyukan mazabun da aka bawa sanatoci uku da 'yan majalisar wakilan jihar. A yayin hakan ne, muka gano cewa taraktocin da za a bawa mazabar Bauchi ta tsakiya karkashin jagorancin Sanata Isa Hamman Misau an siyesu amma ba a bada a inda yakamata ba,"

"Da sa hannun ICPC, muka karba taraktocin tare da adanasu. Munyi bincike tare da bada rahoto. An bukaci Sanatan da ya gyara taraktocin kuma yayi. Shugabanmu ya umarcemu da mu bada su ga shuwagabannin kananan hukumomin da ya dace, mu kuma mun cika umarni."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel