Manyan Bankuna 6 da suka fi samun riba a Najeriya

Manyan Bankuna 6 da suka fi samun riba a Najeriya

Cikin wani rahoto da jaridar This Day ta wallafa a ranar Juma'a, 18 ga watan Oktoban 2019, ta ruwaito cewa, akwai wasu manyan bankuna 6 na Najeriya da suka yi wa sa'o'in su zarra ta fuskar samun riba da yin fice a harkokin kasuwanci.

Manyan bankunan 6 sun yi wa sauran bankunan kasar fintinkau ta fuskar tarin kadarori da kuma kudaden ajiya da aka killace na dai-daikun mutane, gwamnati da kuma na 'yan kasuwa.

A kididdigar da Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar kan shafin sa na yanar gizo a ranar Alhamis ta makon da ya gabata dangane da kafuwar kowane banki na kasar nan, ya nuna cewa wasu manyan bankuna shida sun mallaki kadarori na kaso 59.74 cikin 100 da kuma kudaden ajiya na kaso 60.31 cikin 100 fiye da dukkanin bankunan kasar.

Alkaluman CBN sun nuna cewa an samu karin riba da bunkasar harkokin kasuwanci musamman hannayen jari a bankunan shida idan an kwatanta da kididdigar da aka fitar a watan Yunin 2018.

KARANTA KUMA: Shah Rukh Khan da sauran jaruman fim da kasar Saudiya ta karrama

Duk da cewa rahoton CBN bai fayyace sunayen manyan bankunan kasar ba, jaridar This Day ta wassafa sunayensu kamar haka; Access Bank, Guaranty Trust Bank, Zenith Bank, First Bank of Nigeria Limited, United Bank for Africa Plc da kuma Ecobank Nigeria Limited.

A watan jiya ne majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya ta bukaci CBN ya dakatar da umarnin da ya bai wa bankunan kasar nan na karbe kashi biyu zuwa biyar cikin 100 na tsabar kudin da 'yan kasar suka shigar ko suka fitar daga asusun ajiya da suka haura Naira dubu dari biyar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel