Haihuwar 'ya'ya barkatai rashin fahimtar addini ne - Issoufou

Haihuwar 'ya'ya barkatai rashin fahimtar addini ne - Issoufou

A rahoton da BBC Hausa ta kalato a shafin jaridar The UK Guardian, ta ambato shugaban kasar jamhuriyyar Nijar, Muhammadu Issoufou, yana zayyana dalilin da ya sa ake haihuwar 'ya'ya barkatai a kasarsa babu takaitawa.

Shugaban kasar ya shaidawa manema labarai cewa, rashin fahimtar addinin ne ya sanya wasu iyaye a kasarsa ke haihuwar 'ya'ya tamkar 'ya'yan ridi.

A furucin da ya gabatar wa manema labarai, shugaba Muhammadu Issoufou ya ce ci gaba da yawan haihuwar mutane bila adadin na yi wa kasarsa barazanar haddasa dumamar yanayi da kuma dakushewar tattalin arziki.

An tattaro cewa, jamhuriyyar Nijar wadda kaso 98 cikin 100 na al'ummarta musulmi ne na da yawan jama'ar da ya kai miliyan 22.4, al'amarin da ke nuna karuwar yawan jama'ar daga miliyan takwas tun bayan shekarar 1990 kawo yanzu.

Shugaba Issoufou ya ce "muna samun karuwar jama'a da kaso 4 a duk shekara... yawan jama'a zai karu a shekaru 17 masu zuwa. A shekara ta 2050 za mu iya zama kasa ta biyu mai yawan jama'a a nahiyar Afirka bayan Najeriya."

A shekarar 2016 ne Alkaluman Bankin Duniya suka hasakaka cewa, mace na iya haihuwar yara fiye da bakwai a jamhuriyar Nijar.

Shugaba Issoufou ya ce mai raba gardama wato Al-Qur'ani wanda ya kasance babban kundi da babu bangaren rayuwa da bai tabo ba, ya fayyace yadda ya kamata iyaye su sauke nauyin da ke kansu ga 'ya'yansu da kuma haifar yaran da za su iya dawainiya da su.

KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya da kasar Ghana sun tattauna kan rufe iyakokin Najeriya

"Kafin zuwan musulunci, ana aurar da mata a shekara 18 to amma saboda rashin fahimtar addinin ya sa ake aurar da kananan yara 'yan shekara 12 zuwa 13. Amma idan muka duba me Kur'anin yake fadi ne? Idan mutum ya karanta Alkur'ani zai fahimci cewa littafin yana magana ne a kan iyaye masu kula da 'ya'yansu. Musulunci ya kafa sharadin cewa haihuwar 'ya'ya da yawa ta ta'allaka ne ga ikon dawainiyar tarbiya da ilimantar da su."

Kazalika shugaban kasar ya da cewa, ra'ayinsa kan haihuwar yara da yawa bai ci karo da na malaman addini ba wadanda suke sukar kiraye-kirayen gwamnatinsa na tsari da kuma kayyade iyali.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel