Jakadan Najeriya ya bukaci a tsige gwamnan PDP a arewa, ya bayyana dalili

Jakadan Najeriya ya bukaci a tsige gwamnan PDP a arewa, ya bayyana dalili

Jakadan Najeriya a kasar Trinidad da Tobago, Hassan Ardo, ya yi kira ga majalisar dokokinn jihar Taraba da ta fara shirin tsige gwamnan jihar, Darius Ishaku.

Da yake magana da manema labarai a Jalingo, Jakadan ya ce gwamnan ya cancanci a tsige shi saboda yi wa doka karan tsaye, almundahanar kudi da kuma rashin iya mulki tare da bayyana cewa zai zama rashin kishi idan majlisar ta awar da kai yayin da gwamnan ke cigaba da taka koda.

Mista Ardo ya bayyana cewa gwamna Ishaku ya cancanci a tsige shi saboda cigaba da yin aiki da shugaban kananan hukumomi na rikon kwarya da kuma saba wa umarnin hukumar NFI, wacce ta haramta wa jihohi amfani da asusun hadin gwuiwa.

DUBA WANNAN: FG ta kori mambobin jam'iyyar DPRK 7, ta haramta musu dawowa Najeriya har abada

Wa'adin shugabannin kananan hukumomin jihar Taraba ya kare tun shekaru biyu da suka wuce. Amma, sabanin gwamna Ishaku ya gudanar da sabon zabe, ya cigaba da aiki da tsofin shugabannin kananan hukumomin a matsayin shugabannin rikon kwarya ba tare da amincewar majalisar dokokin jiha ba.

"Kuma kowa ya san cewa wannan gwamnatin, tun kfarkon kafuwarta, na fitar da makudan biliyoyi da sunan kwangila.

"Abun bakin cikin shine bamu ga wadannan kwangiloli ba a ko ina, a cikin fadin jihar Taraba. A duba duk manyan hanyoyin jihar Taraba irin su Jalingo/Pantisawa, Sukundi/Wukari da Yerima/Gassol, duk a lalace suke," a cewar Ardo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel