Bakanike ya damfari dan kasuwa N900,000 da sunan zai masa Visa

Bakanike ya damfari dan kasuwa N900,000 da sunan zai masa Visa

- Hukumar 'yan sandan jihar Legas, ta cafke wani bakanike da take zargi da damfara

- Okoli ya damfari wani dan kasuwa ne da sunan zai samo masa hatimin shiga kasar Korea ta kudu

- Bayan karba kudade kashi daban-daban, dan kasuwar ya gano cewa damfararsa akai

Hukumar 'yan sandan jihar Legas ta cafke wani bakanike mai suna Chukwudi Okoli da laifin damfarar N900,000.

Okoli ya damfari wani dan kasuwa Chibike Asochukwu da sunan zai samo masa hatimin shiga kasar Koriya ta kudu.

Bayan aminta da zai samo hatimin shiga kasar Koriya ta kudun a naira miliyan 1.3, an gano cewa Asochukwu ya fara biyansa N300,000.

KU KARANTA: Dalilin da yasa na wake shugaban kasa Muhammadu Buhari, in ji Alan waka

Mai koken ya bada rahoton cewa, ya kara biyan N450,000 inda daga baya ya dena samun Okoli a waya.

A watan Afirilu na 2019, jaridar City Round ta cewa, Asochukwu ya samu wanda ake zargin Inda yace masa ya samar da hatimin shiga kasar Turkiyya kuma yana bukatar N150,000 don karasawa.

Asochikwu ya bada kudin kuma bai samu Visa din ba, hakan kuwa yasa ya kaiwa 'yan sanda rahoto.

Ya sanar da 'yan sandan cewa, sun fara cinikin ne a yankin Mushin na jihar inda wanda ake zargin ke da shagon siyarda bangarorin ababen hawa.

Jaridar tribune online ta gano cewa, an kama wanda ake zargin ne a ranar 16 ga watan Augusta, 2019 bayan Asochukwu ya kai korafi.

Wanda ake zargin ya kara karbar N650,000 daga Asochukwu bayan da ya yi ikirarin cewa an sace hatimin a Cotonou, jamhuriyar Benin.

'Yan sanda sun kama Okoli da laifin damfara inda suka gurfanar dashi gaban kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel