Dalilin da yasa na wake shugaban kasa Muhammadu Buhari, in ji Alan waka

Dalilin da yasa na wake shugaban kasa Muhammadu Buhari, in ji Alan waka

- Shahararren mawakin Kannywood, Aminuddeen Ladan abubakar, wanda aka fi sani da Alan waka, ya bayyana dalilin da yasa ya wake shugaba Buhari

- Mawakin Kannywood din ya kasance babban dan siyasar PDP, bangaren kwankwasiyya na jihar kano

- Mawakin ya bayyana alakarsa da sarki Bichi da har ya bashi sarauta a kwanan baya

Shahararen mawakin hausa, Aminuddeen Ladan Abubakar, wanda aka fi sani ada Alan waka ya bayyanawa jaridar Daily Trust dalilin da yasa ya wake shugaban kasa Muhammadu Buhari duk da kuwa an san mawakin dan kwankwasiyya ne.

Daga cikin kundin wakokin mawakin akwai: Bakan dabo, Shaahara, Lu’u-Lu’u, Yanar gizo da sauaransu.

KU KARANTA: Lawan ya bawa ministoci wa'adin kare kasafin kudin ma'aikatunsu

“Siyasa ta ni gaskiya ta banbanta da ta wasu. Zabina kuwa ya danganta da nagartar dan takara ne. A takaice dai, ina iya zaben dan takara ne saboda nagartarsa, bana duba da jam’iyyar siyasa. Nayi wa shugaban kasa Buhari waka ne saboda shi ne zabi na. Amma kuma zabina a jihar kano PDP ne.” in ji mawakin yayin da aka tambayeshi dalilin yiwa shuagabn kasa Buhari waka.

Da jaridar Daily Trust ta tambayi mawakin ko abinda ya fada a wakarsa mai suna ‘Lu’u-Lu’u’ ce ta zama gaskiya ganin cewa sarkin Bichi ya bashi sarauta?

Sai mawakin y ace, “Tabbas gaskiya kuka fada. Baiwa daga Allah take gani da cewa nib a daga gidan hamshakai na fito ba. Toh kuwa sarautar da sarkin Bichi ya yi min ta ‘Xan Amanar Bichi’ zan iya cewa kyauta ce daga Allah.”

Dangane da alakar da ke tsakanin Ala da sarkin, Alan y ace: “Ina da alaka mai kyau tsakanina da sarkin tun lokacin da yake da sarautar sarkin dawakin tsakar-gida. Bayan rasuwar Sarki Ado Bayero, wanda shine madubin dubawa na, sarkin Bichi ne ya maye gurbinsa a zuciyata ta.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel