Tashin hankali: Budurwa ta kashe saurayinta akan zoben soyayya

Tashin hankali: Budurwa ta kashe saurayinta akan zoben soyayya

- Wata budurwa ta kashe saurayinta akan zoben auren su da ya bata

- Budurwar ta kashe saurayin ne bisa kuskure bayan yayi kokarin kasheta ta kare kanta

- Alkalin kotun dai ya yanke mata hukuncin shekara goma a gidan yari babu tara babu beli

Rundunar 'yan sandan jihar Legas sun kama wata budurwa mai shekaru 27 wacce aka bayyana sunanta da Blessing Edet da laifin kashe saurayinta.

A yadda rahoton ya nuna, an gurfanar da Edet a wata kotu dake Ikeja a jihar Legas da laifin kashe saurayinta Edet Ebong mai shekaru 33.

An bayyana cewa Edet ta kashe saurayin nata ne bayan rikici ya kaure tsakanin su akan zoben aurensu da ya bata wanda taki sakawa. Yanzu haka dai an yankewa budurwar hukuncin shekara goma a gidan yari.

A cewar jaridar News Telegraph, an zargi Edet da laifin kashe saurayin nata cikin tsautsayi.

Da take bayani a kotu ranar 7 ga watan Fabrairun wannan shekarar, Edet ta bayyana dalla-dalla yada lamarin ya faru.

KU KARANTA: Kasar Uganda ta sanya dokar kisa ga duk mutanen da aka kama suna luwadi

Ta bayyana cewa saurayin nata ya tilasta ta akan ta dafa masa abinci da tsakar dare ita kuma taki ta dafa.

"Bayan na fada masa cewa na gaji sai ya tashi ya tafi ya dafa abincin da kanshi, da zuwa sai yaga zoben da ya bani, sai ya dawo yake tambayata dalilin da yasa ban saka zoben ba.

"Sai ya fasa mudubin dakin mu yayi amfani dashi ya caka mini, jikina na zubar da jini, ina ihu ga makwabta domin su kawo mini dauki," in ji ta.

Ta bayyana cewa a lokacin da suke wannan fada ne sai ta cakawa Ebong wuka a ciki hakan yayi dalilin mutuwar shi.

Da yake yanke mata hukunci, Alkalin kotun ya ce: "Na yankewa budurwar hukuncin shekara goma a gidan yari babu tara ko beli."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel