Bidiyo: Yayana ne ya fara sani na 'ya mace, gashi yanzu har yayi mini ciki, ina mafita - Inji wata budurwa

Bidiyo: Yayana ne ya fara sani na 'ya mace, gashi yanzu har yayi mini ciki, ina mafita - Inji wata budurwa

- Wani bidiyo da yake yawo a kafar sadarwa ta zamani ya bayyana wata budurwa a lokacin da take tona wani sirri na rayuwarta

- Budurwar ta bayyana cewa kusan shekara goma kenan yanzu take kwanciya da yayanta wanda suke uwa daya uba daya

- Ta bayyana cewa yanzu haka har ciki ne da ita kuma na shi ne, bayan haka kuma iyayensu sun matsa musu akan su fito da abokanan aurensu

Wani bidiyo na wata budurwa da ba ta bayyana sunan ta ba, wacce ta bayyana cewa Yayanta wanda suke uwa daya uba daya shine ya fara zubar mata da budurcinta, kuma yanzu haka tana dauke da cikin shi.

A bidiyon, budurwar ta bayyana cewa ta zubar da budurcinta, inda ta fara kwanciya da Yayanta shekara goma da suka wuce a lokacin yayan nata yana da shekara 18 ita kuma tana da shekara 16 a duniya.

Ta ce tun lokacin da suka fara yi a karon farko, sun kasa dainawa yanzu shekara goma kenan kuma har yanzu iyayen su ba su san suna kwanciya tare ba.

KU KARANTA: Ga irinta nan ai: Yadda aka daure wani Sarki a jikin mota aka dinga jan shi layi-layi saboda yaki cika alkawuran da ya dauka kafin a zabe shi

Yanzu haka dai iyayensu sun takura musu akan su fito da miji da mata za su yi musu aure, ita kuma ta riga ta fada soyayyar dan uwan nata.

Budurwar dai ta yi wannan bidiyo ne domin ta nemawa kanta mafita a wajen mutane, inda take tambayar mutane ko akwai wata shawara da za su ba ta dangane da wannan lamari.

Ga dai bidiyon yadda budurwar ta yi bayani a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng