Wani saurayi ya sha mari yayin da ya nemi budurwa ta aure shi a bainar jama'a

Wani saurayi ya sha mari yayin da ya nemi budurwa ta aure shi a bainar jama'a

- Wasu daga cikin samari idan zasu bayyana soyayyarsu ga 'yam mata, sukan nemi waje mara hayaniya ne kuma ni'imtacce don ya zama babban tarihi a rayuwarsu

- Haka kuma gurin yakan kasance na sirri ta yadda koda anyi bari da tayin nasu, ba zai zamo abin kunya ba

- A wani bidiyo da ya dinga yawo a cikin kwanakin nan, wata budurwa ta wanke fuskar saurayin da mari yayin da ya nemi soyayyarta a gaban 'yan aji

Cikin kwanakin nan ne wani bdiyo ke ta yawo a shafukan sada zumunta na wata budurwa da ta wanke saurari da mari yayin da ya kai mata barar soyayyarsa a jami'ar jihar Binuwai.

Wasu mutane idan zasu mika tayin soyayyarsu, sukan shirya guri ni'imtacce ne kuma mara hayaniya don wannan lokaci ya zamo abin tunawa.

Amma wasu mutanen kuwa, sun fi so su bayyana hakan cikin mutane kuma a gaban kowa.

Budurwa ta shararawa saurayinta mari a bainar jama'a bayan ya nemi ta aure shi
Budurwa ta shararawa saurayinta mari a bainar jama'a bayan ya nemi ta aure shi
Asali: Instagram

DUBA WANNAN: Babbar Magana: Majalisar dokokin Legas na shirin bayar da umurnin kama tsohon gwamnan jihar

Abin nan da ya faru ga saurayin, ya nuna cewa, neman soyayya a bainar jama'a ba abu ne da ya dace ba. Komawa inda babu kowa ya fi sirri sannan kuma koda anyi watsi da tayin soyayyar, toh kuwa a sirrance ne. Hakan kuma ba zamo abin kunya ko tozarci ba ga mutum.

A bidiyon, an ga budurwar ta watsawa saurayin lafiyayyen mari a yayin da yake neman soyayyarta a cikin aji a jami'ar jihar Binuwai.

Karara fuskar budurwar ta nuna damuwa da rashin jin dadin aukuwar lamarin inda 'yan ajinsu suka dinga ihu tare da sowa.

Jim kadan kuwa ta wanke masa fuskarsa da lafiyayyen mari sannan daga baya ta yi wucewarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel