Hawan jini da cututtuka 9 da ganyen mangwaro ya ke magance wa a jikin dan Adam

Hawan jini da cututtuka 9 da ganyen mangwaro ya ke magance wa a jikin dan Adam

A kalace-kalacen da muka yi daga jaridar Guardian, mun bankado wasu muhimman tasirai gami da arzikin da Mai Duka ya sanya cikin Ganyen Mangwaro wadanda ke da matukar amfani ga lafiyar dan Adam wajen kawar da cututtuka da dama.

A yayin da binciken masana kiwon lafiya ke ci gaba da bunkasa da kuma kari fadi ta fuskar zamani na kimiyya, ya tabbatar da cewa mafi akasarin magunguna da aka samar da su daga tsatso na itatu sun fi tasiri ga lafiya akan kowane nau'in magani da samo asali daga wasu sunadaran na daban.

Binciken da kwararru na bangaren kiwon lafiya suka gudanar ya tabbatar da cewa, baya ga amfani na 'ya'yan itaciyar Mangwaro akwai kuma tarin arziki da ganyen itaciyar ya kunsa.

Ganyen Mangwaro ya kunshi sunadarai masu tasirin gaske ga lafiyar dan Adam wajen kawar da wasu cututtuka da suka saba addabar al'ummar musamman a wannan zamani. Ire-iren wannan sunadarai sun hadar da; tannins, anthocyanidins, beta-taraxerol, ethyl acetate da sauransu.

A sakamakon wannan arziki na sunadarai da ganyen mangwaro ya kunsa da kuma tasiran su ga lafiyar dan Adam, Legit.ng ta kawo maku jerin wasu cututtuka da idan anyi amfani da Ganyen na Mangwaro akan samu waraka da izinin Mabuwayi.

1. Ciwon Suga

Ana amfani da busasshen ganyen mangwaro da aka nike shi ya zama gari wajen magance cutar suga tun a matakinta na farko sakamakon tasirin sunadaran anthcyanidins da kuma beta-taraxerol da ya kunsa. Kazalika ana kuma jika ganyen magwaro cikin ruwa na kwana guda kana a kwankwadi wannan ruwa domin magance cutar ta suga tun kafin ta ci karfin lafiyar dan Adam.

2. Cutar Hawan

Jini Ganyen Mangwaro ya na da matukar tasiri wajen saukaka cutar hawan jini ta hanyar inganta kuzari na tashoshi da shiyoyi masu aika sakonni na jini.

3. Kasala da rashin karfin jiki

Akan dumama ruwan wanka tare da ganyen mangwaro domin aikata hakan yana kawar da kasala tare da kara kuzari ga dan Adam.

4. Tsakuwar 'Koda

Ana amfani da gari na ganyen mangwaro wajen kawar ta wannan cuta sakamakon narkar da tsakuwar koda tare da tsarkake ta daga cututtuka.

5. Cututtukan tashoshin numfashi

Amfani da markadadde ganyen mangwaro tare da ruwan Zuma yana kawar da duk wata cuta da ta shafi tashoshin numfashi irin su Mura, Tari, Asma, disashewar murya da sauransu. 6. Cutar Atini Akan kwankwadi Garin Ganye Mangwaro da aka jika da ruwa wajen samun waraka daga cutar atini ko da kuwa mai zuwa ce da fitar jini.

KARANTA KUMA: Jihohi 5 da suka fi kwazo a Najeriya - WAEC

7. Ciwon Kunne

Akan dumama ruwan da aka tatso daga jikin Ganyen Mangwaro wajen digawa a cikin kunne domin kawar da radadi da cututtuka da suka shafi cikin kunnen dan Adam.

8. Waraka ga 'Konuwa

Bincike ya tabbatar da cewa ana 'kone ganyen mangwaro kana a yaryada tokar sa domin waraka ga 'konuwa akan fatar dan Adam.

9. Cutar maƙoshi da shaƙuwa

Hayaki daga jikin konannen ganyen mangwaro yana kawar da cututtukan da suka shafi Maƙoshi/Maƙogoro da kuma cutar shaƙuwa.

10. Ciwon ciki

Ko shakka ba bu ana jika ganyen mangwaro a kwana kana a kwankwadi ruwan da sanyin safiya kafin a jefa komai a baka domin hakan yana kawar da cututtuka da dama da suka shafi cikin bil Adama.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel